RAYUWAR MACE MIJI KO UBA

سم الله الرحمٰن الرحيم

RAYUWAR MACE MIJI KO UBA ZANCE NA GASKIYA



WACECE MACE

Ita mace halittar Allah ce, kamar yadda namiji yake, dukkan dabbobi suna da jinsi biyu mace da namiji.

Kuma Allah sabhanahu wata'ala yana raba ayyuka a tsakanin wayannan jinsin (mace da namiji), ta yadda ko wanne zai kasan ce da nasa amfanin, da kuma aiki, dai-dai da abin da ya dace da shi.


Haka zalika suma mutane, suna da jinsi biyu, mutane su ne wayan da suka samo asali daga Adam, wanda shine uban su na farko, kuma namiji na farko acikin muta ne.


Matar sa it a ce hawwa'u, kuma ita ce mace ta farko a cikin muta ne.

Wacce Allah (SWT) ya halicce ta daga shashin jiki na annabi Adam.

Daga Nan, sai suka din ga hai far yaya maza da mata.


Allah (swt) yana cewa; "yaku mutane kuji tsoron ubanjigin ku Wanda ya halicce ku  daga rai daya (Adam) ya halittar masa matar sa daga shi (hauwa'u) ya kuma baza (zuriya) maza da mata masu yawa daga gare su. Kuji tsoron Allah wanda kuke tamabayar (taimako) dashi, kuma (kuji tsoron hakkokin) zumunta hakika Allah me kiwao ne a gare ku (Suratu nisa'i aya ta 1).



MATSAYIN MACE A GUN ALLAH

Allah ya karrama mutane, kuma ya fifta su akan mafi yawan hallitu.

Allah (SWT) yana cewa "hakika mun girmama 'yan Adam, kuma muka dauke su (akan ababan hawa) na sarari da na ruwa, muka kuma azurta su  daga tsarkakan (abubuwa) kuma muka fifita su a kan wasu da yawa daga abin da maka halitta nesa ba kusa ba". [Isra'i :70]


Amma acikin mutane wanda yafi wani tsakani mace da namiji, a gurin Allah, shine wanda yafi wani tsoran Allah.

Allah (SWT) yana cewa; "Ya Ku mutane, hakika mu muka halicce Ku daga namiji da mace, muka kuma sanya ku manya-manyan kungiyoyu da kabilu dan kusan juna, hakika mafi girman ku a gurin Allah, shine wanda ya fiku tsoran sa, hakika Allah masanin sarari ne masanin boye". [ hujrat:13]


RAYUWAR MACE DAGA HAIHUWA

Uwa ita take haifar kowa, daka namiji har mace, don haka idan ta hai fi ya mace, zata ci gaba da rainon ta, uwa ita ce mataimakiyar uba a wajan bawa 'yar ta tarbiyya, a tsahon rayuwa.


Shi kuma uba tun a ciki yake kula da matar da abin da yake cikin ta, bayan an Haife 'yar zai ci gaba da kula da ciyarwar ta, da shayarwar ta, da tufatarwa, da ilimin ta, da tarbiyar ta.


(yana daga cikin aikin uba ya samawa 'ya'ya uwa ta gari, kuma ya kula da ilimi da tarbiyyar ta, ta yadda zata zama kyakkyawar mataimakiya a gare shi).


Bayan mace ta girma, uba zai sama mata miji mai addini (dama me addini, zaka same shi da tarbiyya da hankali), me ilimi, me Sana'a.


Sai ya damka masa Amanar ta, da abubuwan da yake yi (na daga ciyarwa shayarwa tufatarwa ilimantarwa tarbiyantarwa da dai sauransu) don yaci gaba daga inda ya tsaya, tunda yanzu zata bar gurin sa (uba) to koma gurin mijin.


A yanzu shi zai fi kowa kusanci da da ita, da sanin halin da take ciki, sabi da haka; a wannan lokacin shi yafi kowa sanin abin da ya dace da ita.


Kuma dama ya fita hankali, da tunani me kyau, (da san samu ne har da ilimi), zai hanata yin abu mara kyau, kuma ya sanya ta yin abu me kyau, dai-dai gwargwadon iyawar sa.


kuma yana da sana'ar da zai iya warware matsalolin ta, daidai gwargwadon iyawar sa.


DA UBA DA MIJI WA YAFI WANI.


Addinin musulunci ya kangama darajar iyaye,ya daukaka su sama da kome bayan Allah da manzon sa, a gurin kowanne 'da ko 'ya.


Amma kuma a gurin matar aure iyaye suna da wannan matsayin kuwa?

duba da wa'yannan dalilai:


DALILI NA 1:- 

Umarnin miji shine a gaban na uba idan suka ci karo, idan be sabawa Allah ba.


DALILI NA 2:-

Annabi (saw) ya ce; "Da ace zan umarci  wani yayi sujja ga wanin Allah, da na umarci mata ta yiwa mijin ta sujjda"

ibn majah ya rawaito shi (1853)



Amsa:

DALILI NA 1:

UMARNIN MIJI AKAN NA UBA



Ba iya biyyya kadai make yiwa iyaye ba, daga ciki akwai; kai su saman kowa a fannin kyautatawa, tausayawa, temakawa, da sauran su.


A fanin girmamawa kuma daga allah sai manzon sa sai su.


Idan miji ya dauke wani fanni na karfin iyaye, a fannin bin umarnin sa sama da na su, ba zai iya dauke sauran ba, balle ace ya fi su.


Amma shima yana da nasa matsayin me girma.


Addinin musulunci yana shinfida mana tsarin rauyuwar da zamu ji dadi, mu zauna lafiya a duniya, idan muka bi, a lahira kuma mu samu babban rabo.

(Riba biyu kenan)


 Allah ya tsara mata tabi umarnin mijin ta, don ya samu saukin sauke nauyin da aka dora masa. (Wanda a da mahaifinta shi yake yi) dole ta bashi hadin kai, tare da biyyayya, kamar yadda zata yiwa baban ta.


Kuma uba bai kamata yayiwa miji shishshigi a al'amuran sa ba, tunda ya riga ya damka masa amana, sai dai idan yaga cutarwa.


kamar misalin; uban da ya kai yar sa makaran ta, sai yi dinga yi musu shishshigi, tabbas! baza a zauna lafiya fa.


A misali:

1- a makaranta malamin su yace: "zasu yi jarrabawa"

sai uban yace: "a'a kar kiyi, yi aikin gida ki kai masa".


2- ko malami yace "karfe 8:00 zaki dinga zuwa makaranta" 

 Uba kuma yace "ki dinga tafiya karfe 10:00"


3- ko malami yace "rana kaza hadda"

  Uba shi kuma yace a'a sai rana kaza, ko kuma biye zaki basu


To idan yana haka, yarsa zata daku ne a makaranta, idan suka ga ba zasu iya ba, su kore ta.


Anan dole umarnin malami shine a saman na uba, dun samun maslaha, ba dan yafi shi daraja ba.

(Wannan haka mutane suke don samun masalaha)


Haka shima aure, duk da cewa ba iya makaranta bane, amma akwai ilimantarwa a ciki.


Idan uba ya kai yar sa gidan aure, sai ya dinga yiwa miji shishshigi, tabbas shima ba za'a zauna lafiya ba.

  Idan yana haka, yar sa zata wahala, idan mijin yaga bazai iya ba, ya sako masa ita.


Anan dole umarnin miji shine a saman na uba, dun samun maslaha, ba dan yafi shi daraja ba.

(Wannan umarni ne na Allah)


DALILI NA 2:

DA ZA'A UMARCI WANI YA YIWA WANI SUJJADA BAYAN ALLAH...


Annabi (saw) ya ce; "Da ace zan umarci wani yayi sujja ga wanin Allah, da na umarci mata ta yiwa mijin ta sujjda"

ibn majah ya rawaito shi (1853)


Wannan hadisin yazo da zance me girma.

Allah kawai ake wa sujjada. da za'a yiwa wani na biyu, da miji ne, ba iyaye ba. Kenan miji yafi uba, yafi iyaye, dan ba'ace su ba, sai aka ce shi.


Wannan hadisi ba ya Nuna miji yafi uba ko iyaye bane, don kawai su ba'a kwatanta su da wannan ba.


Dalili shine annabi (saw) ya fi miji da uba daraja, da cancantar biyyaya, a gurin kowanne musulmi mace da namiji, daga Allah sai shi.


Da ace haka ne, da annabi shi yake da cancantar daraja, da girma bayan Allah.


Amma kuma shima ba'a kwatanta shi da wannan zancen ba.


Hakan ya nuna; wannan ba ma'auni bane, Wanda za'ayi anfani da shi wajan kwatanta matsayin wani yafi wani ba.


Sai dai kawai, yana nuna mutukar muhimmancin biyayyar mace ga mijin ta.



HAKKIN MIJI BAYA DANNNE NA IYAYE

Kowa da nasa hakkin, daya baya danne daya.

Hakki iyaye da girman su, Abu me babba da muhimmanci a gurin Allah, saboda haka Allah Madaukakin Sarki ya hada shi da hakkins a a wurare da dama a cikin alqur’ani mai girma.


Miji ba ruwan sa da hakkokin uba (ko iyaye), sai dai yayi umarni da'a cika su.


Haka zalika uba (ko iyaye)  ba ruwan su da hakkokin miji, sai dai suyi umarni da a cika su.


MIJINKI BAI FI UBAN KI BA

Har abada a gurin kowa bayan Allah da manzon sa, babu kamar iyaye.


Babu wani Wanda ya cancanci biyayya da kyautatawa, bayan Allah da manzon sa sama da iyaye.


Shi yasa Allah ya sanya da'ar iyaye a gaban kome, bayan da'ar sa.


Ba ayi wata da'a ko ibada, ko aikin lada da Allah madaukakin sarki ya ba shi muhimmanci a cikin alkur'ani (bayan kadaita Allah) kamar yadda ya bada muhimmanci ga da'ar (biyayya da kautatawa) iyaye.


Alla Subhanahu wa Ta’ala yace:


“Ku bauta wa Allah, kada ku yi masa shirka da komai. Kuma ga iyaye ku kyautata.” [Suratun Nisa’i: 36]


Sannan wata rana an tambayi Manzon Allah (SAW) game da mafiya soyuwar ayukka a wurin Allah, sai ya amsa da cewa:


“Yin Sallah a kan lokacinta. Aka ce sai me? Yace: “Yin biyayya da da’a ga iyaye.” Aka ce sai wane? Yace: “Yin Jihadi a kan tafarkin Allah.” [Buhari da Muslim]



Babu lefin da ya kai sabawa iyaye bayan shirka


 An rawaito daga Abu Bakra, Allah ya yarda dashi, Annabi (saw) cewa shi yace: “Bana baku labarin mafi girman Manyan lefuka ba”sau uku.sai muka ce: "eh ya Manzon Allah", 

ya ce: “Shirka da Allah, da kuma Sabawa Iyaye", yakasance yana Kashingide sai ya mike ya Zauna, kuma y ace: "Ku saurara Maganar Zur da Shaidar Zur,” bai gushe ba yana maimaita ta ba, sai da muka ce: "ina ma dai yayi shiru".    

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]



DA KA KARSHE

~Ba dai-dai bane don zaka fadi darajar miji a gurin mata, sai ka kaskanta darajar iyaye.

hakkin su baya danne na miji, na miji baya danne na su.

Ko wanne da nasa matsayin amma iyaye sune a gaba.


~umarnin miji yana zama a saman na uba, dun samun maslaha, ba dan yafi shi daraja ba.


~Ba iya biyyya make yiwa iyaye ba daga ciki akwai kai su saman kowa a fannin kyautatawa, tausayawa, temakawa, da sauran su.

A fanin girmamawa kuma daga allah sai manzon sa sai su.

Idan miji ya dauke wani fanni na karfin iyaye a bin umarnin sa sama da na su, ba zai iya dauke sauran ba balle ace ya fi su.


~Kuma wannan fadar annabi cewa "da ya umarci mace tayi sujjada ga miji",  ba ma'auni bane Wanda za'ayi anfani da shi wajan kwatanta matsayin wani akan wani, ko darajar wani yafi wani ba.

Da ace haka ne, da annabi shi yafi cancantar wannan, don yafi kowa daraja da girma bayan Allah.

Sai dai kawai yana nuna mutukar muhimmancin biyayyar mace ga mijin ta.

Alhamdullah 
B*shakz fadakarwa B*shakz

Comments

Popular Posts