Musha dariya part 4

  B shakz

Musha dariya part 4

21- WANI BATURE NE DA BAYERABE 


Wata rana bature yaje kasar yarbawa, sai yaga wani mutum da tsagunan na fuska. 


 sai baturen nan yaje wajen mutumi nan, yana shafa masa fuska. sai ya kalle mutumin nan yace masa: "na you fight with tiger ne". 

(Kayi fada da damisa ne). 


 sai yace masa: "no i fight with ubanka ne" 

 (a'a nayi fada da ubanka ne)


 sai bature yace: "wow ubanka is berry dengerous animals".

 (kai ubanka muguwar dabbane) 


Hhhhhhhh 


 DATTIJO ME NOMA 

Wani dattijo ne yayi niyyar Noman gyada, da damina. 


 Ranar da aka yi ruwa mai yawa, sai ya je Gona, ya na fara huda, sai kawai ya ji ance: "kai Ku taya shi mana"!!! 


 Kawai sai yaga an hude gonar baki daya, washegari ya zo, da nufin yayi shuka, yana sarawa zai fara shuka, sai ya ji an ce kai: "Ku taya shi mana"!!! 


Sai ya ga, an shuke gona duka.


 Haka dai! duk lokacin da yazo aiki a gona, sai ya ji ance: "kai Ku taya shi mana".


 Har sai da Gyada ta isa roro, ya zo ya fara aiki, sai ya ji an ce: "kai ku taya shi mana". 


 Nan take aka gama aikin roron Gyada, Sai ya dan dauki daya, ya ci, Kawai sai ya ji an ce: "kai ku taya shi mana". 


 Nan da nan suka cinye Gyada, 


Ashe aljanu ne. 


 kai ku tayani mana!!!! Amma fa dariya


Hhhhhhh


Alhamdlillah


Ku kasance damu don nishadantarwa, fadakarwa, da ilimantarwa.

Comments

Popular Posts