TATSUNIYAR DAN AUTA

B*shakz tatsuniyoyi B*shakz

TATSUNIYAR DAN AUTA

 Wani mutum da matar sa suna da yaya biyu duk maza.

Sai wata rana mutumin nan ciwon ajali ya kama shi, sai yayi wa babban dan sa wasiyya yace; "kaga yanzu mutuwa zan yi, amma ko bayan ba raina ka kula da Dan auta, duk me yake so kayi masa".

Sai babban Dan nasa yace "to baba"


Shi kenan banban nasu ya mutu, ya bar musu Runbun abin ci, da kuma shanu.

Anan sai wata rana itama Babar su ciwon ajali ya kama ta, sai ta yiwa babban Dan wasiyya tace; "kaga yanzu mutuwa zan yi, amma ko bayan ba raina ka kula da Dan auta, duk me yake so kayi masa".

Sai yace "to inna"


Shike nan ta mutu, ta bar musu rubun abin ci, da kuma shanu.


Suna zaman su su biyu, sai wata rana Dan auta yace "unhum! Unhum!"

Sai yayan nasa yace "Dan auta menene"?

Sai yace "ni so nake na kone Runbun nan"

Sai yayan nasa yace; "yanzu in ka kone mana Runbu, a ina zamu samu abincin da zamu ci"?

Sai Dan auta yace "to ba baba da inna sun ce duk abin da nake so ka bani ba"?.

Shi kenan ya rabu da shi, Dan auta ya kone Runbu, suka koma shan nonon shanu, suna yankawa suna ci.


Ana nan wata rana sai Dan auta yace; "Unhum!! Unhum!!"

Sai yayan yace; "Dan auta menene?"

Sai yace "ni so nake na kona shanun nan"

Sai yayan yace "to yanzu in ka kone mana shanu me zamu ci"

Sai yace "to ba baba da inna sun ce duk me nake so ka ba ni ba?"

Shi kenan ya rabu da shi Dan auta ya kone shanu.


Suna zaune a haka, daga su sai gidan su.

Wata rana sai Dan auta yace; "Unhum!! Unhum!!"

Sai yayan nasa yace "Dan auta menen?"

Sai yace "ni so nake na kona gidan nan"

Sai yayan nasa yace "yan zu idan ka kone gidan nan, a ina zamu zauna?"

Sai yace "to ba baba da inna sun ce duk me nake so ka ba ni ba?"

Shi kenan ya rabu da shi, Dan auta ya kone gida.


Suka koma ba su da gida suka fita sai suka zo wucewa ta gurin wata rijiya, sai suka ga wata mata tana diban ruwa.

Sai Dan auta yace yace; "Unhum!! Unhum!!"

Sai yayan nasa yace "Dan auta menen?"

Sai Dan auta yace "so nake na jefa wannan matar rijiya"

Sai yayan yace "yanzu idan ka jefa ta ta mutu fa, muma fa a kashe za'a yi"

Sai yace "to ba baba da inna sun ce duk me nake so ka ba ni ba?"

Ai kuwa Dan auta ya jefa  ta, fadawan sarki suka biyo su, amma su Dan auta suka gudu, Fadawan nan suka duba basu gan su ba, ashe sun haye wata bishiya, Allah ya sa matar nan bata mutu ba, aka dauko ta daga rijiyar.


Suna zaune akan bishiyar nan, basu sani ba ashe bishiyar kofar gidan sarki ce.

Can sai sarki ya fito shan iska, sai aka yi masa shinfidu ya zauna a karkashin bishiyar.

Su Dan auta suna kan bishiya suna kallon sarki.

Can sai Dan auta yace "Unhum!! Unhum"

Sai yayan nasa yace "Dan auta menen?"

Sai yace "ni so nake na yi kashi a kan sarkin nan"

Sai yayan nasu yace "yan zu idan kayi kashi akan sa kashe mu za'ayi".

Sai yace "to ba baba da inna sun ce duk me nake so ka ba ni ba?"

Shikenan ya rabu dashi, Dan auta yayi kashi akan sarki.

sarki yaji Abu a kan rawanin sa, ya yi tsammanin dan itaciyar ne ya fado, yaji dadi zai sha dan itaciyar, ya sa hannu da niyar dauko shi daga kansa, sai ya dauko kashi.

Sarki ya daga kai, sai yaga su dan auta, nan da nan yace da fadawa su sare bishiyar.

Kan kace me an sare bishiya, su Dan auta suka duro suka fara gudu, fadawa suka bi su, su Dan auta  suka gudu suka bar gari, suka je wani gari.


Sai suka je gidan wata tsohuwa suka ce "dan Allah ta basu dama, ko a soron ta ne su kwana".

tace "to, amma akwai dodo a garin, kullum yana zuwa da dare ya cinye mutane, in suka kwana a soro zai cinye su, amma ga daki su kwana aciki". 

Suka ce sun gode, bayan kwana daya sai Dan auta yace "Unhum!! Unhum"

Sai yayan nasa yace "Dan auta menen?"

Sai yace "ni so nake na kwana a soro"

Sai yayan nasu yace "yan zu idan ka kwana a soro dodo zai cinye ka".

Sai Dan auta yace "to ba baba da inna sun ce duk abin da nake so ka bani ba"?.

Sai ya rabu da shi, Dan auta yaje ya samo dawatsun wuta, ya samo itatuwa, ya ajiye.


Dare nayi, yaje soro, ya kunna wuta ya saka duwatsun wutar nan a ciki, suka yi jazur, sannan yayi shinfida ya kwanta.


Can sai ga dodo ya zo, yana yiwa kansa kirari, yana cewa;

"in dodo ni dodo,

Ni dodo iya na baba

Sarakan bana hanbori hanbori'


Sai Dan auta yace;

 "Ni auta ni auta

Ni autan iya na baba

Sarakan bana hanbori hanbori"

Sai ya dauko garwashin dutsen wutar nan da yayi jazur, ya jefawa dodon a baki.


Sai dodo ya hadiye, ya cigaba da yiwa kan sa kirari.

Dan auta yana kara jefa masa dutsen, shima yana yiwa kansa kirari.


Haka har ya jefa masa gaba daya duwatsun, dodon yana hadiyewa, dutsen nan ya cika cikin dodo, can sai cikin dodon ya ce foosss! Ya fashe.


Dodo ya fadi matacce, Dan auta yaje gurin dodon nan ya yanke jelar sa, ya barshi anan yaje yayi baccin sa.


Da gari ya waye mutanen gari  suka ga gawar dodo, amma an yanke jelar sa, labari ya bazu a gari, an kashe dodo.


Har labari yaje gun sarki, sarki yace jelar dodon tana gun wanda ya kashe shi, don haka duk wanda ya kashe dodon nan, zai bashi rabin gari, da rabin dukiyar sa.


Ko da jin haka, sai mutanen gari kowa ya dinga zuwa, wani da jelar kura, wani ta giwa, wani da jelar sa, wani da jelar rago, wani da jelar bunsuru, wani jelar kare, duk suna cewa su suka kashe dodo.


Su Gizo kuwa da jelar bera ma ya je, yace ita ce jelar dodon, don a bashi rabin gari da rabin dukiyar sarki.


Ana cikin magana da gizo  sai aka ga Dan auta ya zo da jelar dodo, ai kuwa kowa yace wannan tabbas ita ce jelar dodo.


Mutane sukai ta mamakin wannan Dan karamin yaron taya ya kashe dodo?.


Sarki ya bashi Rabin gari, da Rabin dukiyar sa, ai kuwa suka zauna shi da yayan sa, da tsohuwar da ta basu gurin kwana, sannan yasa aka nemo matar nan daya taba jefawa rijiya, ya bata hakuri, ya bata dukiya me yawa, ta yafe masa, tayi masa addu'a.


Shekenan Dan auta ya zama me hankali, ya daina rashin ji 


Shikenan, Kurunkus!!!


B*shakz tatsuniyoyi B*shakz

B*shakz tatsuniyoyi B*shakz

Comments

Popular Posts