TATSUNIYAR GWAI-DA-YARA
TATSUNIYAR GWAI-DA-YARA
gata-nan gata-nanku!!!
gata-nan gata-nanku!!!
gata-nan gata-nanku!!!
Akwai wani mutum yana da matan sa su hudu, dukka ninsu suka sami ciki alokaci daya.
da watan su ya kama suka haifi ya'ya duka Mata, bayan mako guda na al'ada ya radawa uku daga cikin yaranan sunaye.
'Daya sunanta halima, daya jummai, ta ukun kuma Aisha, amma sai yaki radawa yar matar sa daya suna.
sai mahaifiyar ta ta tambaye shi “me yasa ni ba zaka sawa 'yata suna ba?”
yaki bata amsa, sai kawai yace mata; Ai yana sane zai rada Mata suna.
haka dai tarinka tuna masa, har wata rana acikin gatse yace: “kije sunan ta gwai-da-yara”
kwance tashi, yaranan hudu suka girma, suka isa aure, shi kuma ya tsaya ya tabbatar halima da jummai da Aisha kowacce tasami mijin aure, watau banda gwai-da-yara.
yayi haka ne sabo baya son mahaifiyar ta, da mahaifiyar ta taga haka, sai ta durku sa tace dashi: “shin mai gida me yasa ba zaka yi wa 'yata aure ba, kamar yadda ka yiwa Yan’uwan ta ba?”
sai ya dubeta yace “ki gaya Mata ta rinka bina gona a daji".
Uwar gwai-da-yara kuwa bata yi jinkiri ba wajan sanar da 'yarta abun da Mai gida yace ta gaya mata ba.
haka kuwa akayi duk sanda uban zaije daji sai tabishi, kullum haka abu kamar da wasa ya dore.
Wata rana suka je tsakiyar daji, sai wani bakin maciji ya wuce sululu tagaban su, sai uban yace da gwai-da-yara; "ga mijin ki nan ki bi shi duk inda ya dosa".
To, sabo da biyayya irin wadda taga uwar ta take yiwa mahaifin ta, sai tace dashi; “to baba na gode”
Daga nan ta dunga bin macijin, ba tare da tsoro, ko shakka ba.
To ashe shi ba maciji bane mutum ne,kuma dan sarki, da ya ga yarinyar na bin sa kamar yadda uban ta yace tayi, kuma ya lura uban yarinyar ya Kama gaban sa.
Sai ya rikida ya koma mutum sai ya tambayi gwai-da-yara “baiwar Allah me kika zo yi anan"
Ganin abun da ya faru sai tsoro da dimaucewa suka sa ta kasa yi masa bayani, ya dai ji uban ta yace; "bi macijin nan shine mijin ki".
Da dan sarkin nan ya Lura da dimautar da gwai-da-yara take ciki, sai yace da ita; “kada ki damu kanki, kima daina jin tsoro, muje garin mu a daura mana aure, ai mahaifin ki ya bani ke".
Sai shi da ita suka Kama hanyar garin mahaifin sa, har suka isa, sai taga ana faduwa kasa ana gaishe shi, da ya shiga gida sai ya kai ta ta huta.
sai yace suje wurin mahaifin sa, suka je suka gaida sarki, sai sarki ya tambayi 'dan sa; "yariman Babba lafiya na gan ka da wannan yarinya wacece"?
sai yace dashi "ka dade Mai duniya, wannan yarinyar Dana zo da ita, ina neman izinin ka in aure ta, nan take kuwa sarki ya amince, bayan kwana biyu aka daura musu aure.
Sarki ya kawo dukiya Mai yawa, ya bawa dan sa da surukar sa,. Dan sarkin nan kuwa ya debi dukiyar yaje daji dai-dai inda surikin sa yabar yar sa, ya kangama gida suka tare.
Suna nan wata rana, baban ta yaje gona, sai ya tarar da wasu Mata suna Jan ruwa a arijiyar da ke kofar katafaren gidan nan, wadannan Mata kuyangun gwai-da-yara ne, matar yarima babba.
Ya roke su ruwan sha amma suka hana shi, tare da bayanin cewa “ko zamu baka sai mun cika duk randunan gwai-da-yara".
Daman gwai-da-yara tasaba takan leka kofar gida ta taga, da ta leka sai ta hango mahaifin ta yana magana da yan aikin ta, sai ta kira daya ta tambaye ta :“me mutumin nan yake cewa ne?"
Sai yar aikin tace; “yace mu bashi ruwan sha ne, mukace sai mun gama cika randunan ki."
Sai gwai-da-yara tace; "kuba shi ruwa ya sha, idan ya sha kuma kuce ya shigo."
Bayan mahaifin gwai-da-yara ya sha ruwa, sai yaji acikin ladabi daya daga cikin kuyangun nan tace; “gwai-da-yara matan dan sarki tace ka shiga gidan nan".
Sai ko ya shi ga ya zauna a zaure, yana jira ya ga abun da zai faru, kafin ta aika a gayawa Mai gidan ta mahaifin ta yazo, sai taji motsin shigowar mai gidan nata gida, bai tsaya a zaure ba, koda yake yaga bakon mutum, Amma bai san ko wanene ba.
sai gwai-da-yara ta tunkari mijin ta bayan fadawan sa sun tsaya a soro tace; "yaya ka wuce mahaifi na baka gaida shi ba?"
Sai yace; “yana ina? ban gan shi ba."
Acikin karairaya irin ta Matan da suka iya kissa, tace dashi; "ai shine a zaure, ai gara ku gaisa."
Sai mijin yaje suka gaisa, aka ba shi masauki irin ta alfarma, yayi wanka da ruwan dumi, ga tufafi sababbi da aka kawo masa, ya zaba ya saka.
Bayan mahaifin gwai-da-yara ya kara hutawa, can da la,asar surikin da 'yar sa suka kawo kyan-kyandi gomiya daya da biyar, cike da tufafi da kudi, suka bashi.
wasu kayan na shi ne, wasu kuma tsarabar da zai kaiwa matan sa ne, yayi mamaki da godiya, bayi da fadawa suka dauki kayan, aka raka shi har gida.
Da ya Kai kayan tsarabar ya yiwa matan gidan bayani, sai suka ce; “wannan tsarabar yayan mu ne suka aiko, wa zai ba gwai-da-yara arziki haka?"
haka dai! suka rabe kayan suka Hana mahaifiyar gwai-da-yara.
Bayan yan kwanaki sai mahaifin su ya shirya zai ziyarci sauran yayan sa, Wato jummai da Aisha, da halima.
A gidan halima ya tarar ita da mijin ta basu da abinci, banda birrai da beraye ba komai, sabo da tsananin talauci, jikin ta yayi kirci, bata da ko sabulun wanka, hatta tabarman Kwanciya bata da ita.
Bayan ya gama ziyarar su zai tafi, sai ta kunshe masa kan biri, da jelar beraye a tsumma ya kaiwa mahaifiyar ta tsaraba.
da uban yaje gidan jummai, sai ya tarar da su basu da wani abinci, sai ganyen radiya, da gautan daji, da tsamiyar kasa, babu rumbu balle masussuka a gidan su.
bayan ya gama ziyarar ta, ita da mijin ta suka roko gaskami daga makwabta, tasa a wani kata don ya kaiwa mahaifiyar ta tsaraba.
Aisha ce mijin ta yake da dan karfi, domin dan abun da yake dashi, har dusa yakan samo ta tuka musu tuwo, wani lokacin kuma sukanci zogale da Wake, kuma tana da Zane sakakke da turmi da ta baryar yin aikatau.
da zai tafi gida ta debo dusa mai yawa ta bashi ya kaiwa mahaifiyar ta tsaraba.
Da Uban ya koma gida, sai yace da matan nasa; “inaso duk yaran nan kowacce tazo da mai gidanta, ranar laraba mai zuwa."
Aka aika musu, kowacce taci ado, dai-dai arzikin ta, ta taho tare da mijin ta.
gwai-da-yara ce ta fara zuwa tun da sanyin safiya, ta shiga dakin mahaifiyar ta dake kusa da kofar gida, sauran matan gidan basu san ma ta iso ba, kuma tare da tarin kyankyandi cike da dukiya mai yawa.
sauran kowacce tazo dukkanin su abin tausayi, suna fama da rama da gajiya, gashi basu da suturar kirki.
Kowacce ta shiga ga mahaifiyar ta, wai suna jiran ganin a mugun halin da gwai-da-yara da mijin ta suke ciki.
Can kuma sai ga mazan su ma sun iso, mijin halima ya sha lagen wani luru daya a huje, mai gidan jummai kuma ba komai ajikin sa sai bante.
mijin Aisha ne mai dama-dama domin yasa yar shara, wadda ya aro a wurin abikin sa.
mijin gwai-da-yara kuma ya tunkaro tun yana nesa kamshin turare ya cika gari, fadawa suna gaba, masu algaita na busawa, baka da nata kida, sai kirari akeyi masa ana cewa; "lafiya yarima babba dan sarki, angon gwai-da-yara.
Bayan ko wacce ta fito tare da mijin ta, sai iyayen mata suka kama kuka, da nadamar halin da jummai da halima da Aisha da ake so suka shiga a gidajen auren su.
Nan take! suka bama mahaifiyar gwai-da-yara hakuri bisa matsa lamba da wulakanci da suka dinga yi mata a baya, ita kuwa tace ta yafe musu.
gwaidayara ta kawo tufafi, da kayan abinci, da abin zaman gari, mai yawa taba yan-uwanta kowacce da mijin ta.
Ta kirawo kishiyoyin uwar ta, ta basu kayan tsaraba wadanda basu taba jin labarin irin su ba, suka yi godiya.
daga nan kuma uban yace ba sauran a wulakanta kowa agidan sa.
KURUNKUS!!!!.
DARUSSA ACIKIN TATSUNIYAR
~Hakuri
~Hakuri da biyayya ga iyaye, da jurewa kuntatawar su abune mai kawo arziki da nasara a rayuwa.
~illar nuna bambanci tsakanin 'yaya mutum ya Haifa.
~nuna gata da shagwaba ga yaro wata hanya ta koya masa sangarcewa da lalacewa da talauci da shiga halin danasani.
~Allah shine yake azurtawa kuma yake talauta wanda yaso.
B*shakz tatsuniyoyi B*shakz

Comments
Post a Comment