HIKAYOYIN SHEHU JAHA
HIKAYOYIN SHEHU JAHA
B*shakz hikayoyi B*shakz
HIKAYAR SHEHU JAHA
YAYA NA GA KANA TAUSAYA MASA?
Wani mai kudi ya gayyaci Shehu wata walima da ya shirya, sai ya kawo masa wani karamin dan akuya gasasshe.
Sai Shehu ya rika ci da sauri, da sauri, sai mai walimar (wanda mutum ne marowaci), ya ce da Shehu: “Yaya na ga kana yi masa cin rashin imani, ko uwarsa ta tunkuye ka ne?”
Sai Shehu ya ce “yaya na ga kana tausaya masa, ko uwarsa ta shayar da kai ne?”
Hhhh
HIKAYAR SHEHU JAHA
Wata rana Shehu yaje kasuwa, sai ya hadu da wani mutum, shi kuma ya siyo tangaram cike da buhu.
Sai yace ma shehu; "ka daukar man kayannan nawa, ka kaiman gida, ni kuma zan sanar dakai wasu abubuwa guda ukku da zasu amfane ka, har karshen rayuwarka."
shehu yace ya yarda.
Suna cikin tafiya, har sunyi kashi daya cikin ukku na tafiyarsu, sai shehu yace; "ka fada min yanzu".
Sai mutumin yace; "na daya duk wanda yace maka da ƙkoshi gara yunwa karka gaskata shi".
Shehu yace; "to na biyu fa"?
Sai yace "duk wanda yace maka da tafiya kan abin hawa, gara tafiya a ƙkasa kar ka gaskata shi".
Bayan sun isa kofar gidan mutumin sai shehu yace; "ka fada min gudan".
Sai yace "duk wanda yace zan biya ka ladan daukar kayan nan, karka gaskata shi"
Da jin Haka, sai kuwa Shehu ya buga Kayan tangaran dinnan a kasa, yace da Mai Kayan; "Duk Wanda yace maka cikin buhun Nan akwai tangaran Mai kyau, kada ka gasgata shi".
Hhhh
GIDAN CIN ABINCI
Wata rana Shehu yaje wani gari, sai ya tarar da wani gidan cin abinci an rubuta ‘'kazo kaci abinci, jikan ka ya biya maka'’
Kawai Shehu yana ganin haka yace a ransa “af ga banza tazo, inci kuma jika na ya biya min”
Kawai sai ya kutsa kai ya shiga, Aka kawo masa abinci ya ci yayi nak! Sai ya tashi zai tafi, sai aka ce “malam kawo kudi mana”
Sai Shehu ya bata rai yace “ba kunce kowa yaci jikan sa zai biya masa ba?”
Sai suka ce “eh haka ne abin da yasa muka tambaye ka, zaka biya wa kakan ka ne, kai ma idan jikan ka yazo sai ya biya maka."
Hhhhh
ME YA SHAFE KA?
Wani mai karambani ya taba zuwa wajen Shehu ya ce da shi: “dazu na ga wata dakwalwar kaza dafaffiya a cikin wani kwano, wasu mutane biyu suna tafe da ita.”
Sai Shehu ya ce: “To me ya shafe ni?”
Sai mutumin ya ce: “Ai gurinka suka taho.”
Sai kuma ya ce: “To me ya shafe ka?”
Hikayar shehu jaha.
Wata rana Shehu ya yi shirin tafiya gona, sai ya yi wa matarsa bankwana.
sai ta ce: “amma ba ka ce insha Allah! Ba.”
Ya ce: “ba sai na fada ba, saboda ni dai ne zan je gonar nan, kuma nayi niyyar tafiya, hasali ma daga nan gurin gonar na nufa, kin ga babu bukatar dole sai nace insha Allahu.”
Ya yi tafiyarsa gona, can sai hadari ya gangamo aka fara ruwan sama kamar da bakin kwarya, Shehu ya nemi guri ya fake, aka yi ta ruwa bai dauke ba har dare yayi.
sai kawai Shehu ya kama hanyar komawa gida, duk da ruwan na dukan sa kafin ya dawo gida duk ya jike jagab!.
A kan hanyarsa ta dawowa gida sai yaci karo da wasu gungun sojoji, sun yi dimuwa suna neman hanya.
Suka nemi taimakon Shehu da ya nuna masu hanya, Cikin fushi Shehu yace “kuna ganin ruwa ya bani kashi, maimakon ku bar ni naji da abin da ya dame ni, shine don rashin imani irin naku, zaku dame ni da tambayoyin banza.”
Wannan Magana ta shehu ta batawa sojoji rai, kwarai da gaske, don haka suka kama shi suka yi masa dukan kawo wuka.
Da kyar da jibin goshi Shehu ya iso kofar gida, sai ya samu kofa a garkame! An kulleta ya bubbuga kofar don a bude masa.
can sai yaji muryar matarsa tana cewa: “wanene?”
Sai ya kwantar da murya ya ce: “ni ne mijinki INSHA ALLAH!”
Hhhhh
TSAYA NAN NA GWADA MAKA YADDA ZAN YAUDAREKA
Wata rana shehu yaji wani yaro yana kirarin cewa shi babu wanda ya isa ya yaudare shi, ko ya damfare shi.
Sai yace dashi; "To tsaya nan, ni kuwa bada jimawa ba zan gwada maka yadda zan yaudare ka."
Sai ya tafi ya bar shi a wajen, yayi ta tsayuwa awowi masu yawa, amma bai ga alamar shehu ba, har dai ya gaji da tsaiwa, sai ya rika lanlankwashewa.
Da abokan sa sukazo wucewa sai
suka ce dashi; "kai kuwa tsaiwar me kakeyi a nan"?
Sai ya basu labarin abinda ya wakana, sai wani abokin sa ya tintsire da dariya yace dashi; "Amma ka cika sakarai, To ai gashi nan ya yaudare ka, dabara ta kubuce maka".
Kai jama’a, shehu sai Allah. Ya wuce tunanin jama’a.
Hhhhh
ALKALANCIN SHEHU.
Wata rana wani mutum yayo itace a daji, yana kan hanyar sa ta dawowa sai suka kwance suka zube, ya rasa yadda zaiyi.
Sai ga wani mutum yazo zai shige, sai mai itace yace “Malam ka taimaka ka taya ni mu tara itacen nan mu daure.”
Mutumin yace “idan na taya ka me zaka ban?”
Mai itace yace "zan baka 'babu"'.
Mutumin ya taya shi suka daure itace, mutumin yace “bani abinda kace zaka bani”
Mai itace yace “ai babu nace zan baka”
Mutumin yace “to bani babun”
Ai ko sai rikici ya balle a tsakanin su, har ta kai su ga alkali suka yiwa alkali bayani, alkalin yayi dabaran su na alkalai, amma ina mutumin yace dole sai an bashi babun sa.
Sai mutane suka bawa alkali shawara a nemo Shehu, domin shi kadai ne zai iya warware wannan shari’a.
Aka nemo Shehu, da yazo aka shimfida masa darduma ya zauna, mai kara yayi bayani, wanda ake kara ma yace gashi gashi.
Ko da Shehu yaji haka sai ya cewa mutumin “kanaso a baka babun ka ko?”
Mutumin ya amsa da “eh”
Kawai sai Shehu ya daga dardumar da yake zaune a kai ya cewa mutumin ya leka.
Mutumin nan ya leka.
Sai Shehu yace “me ka gani?”
Mutumin yace; "babu"
Sai Shehu yace "to dau babun ka kayi tafiyar ka kana wahalar da sharia".
Hhhhhh
MASU GEMU MA YA SASU BACCI BARE JARIRAI
Wata Rana Matar Shehu ta zo wajensa cikin dare hankalinta atashe, tana cewa da shi; "Na Rasa abin da yasami yaron nan, Babu abin da yakeyi ban da Kuka ako da yaushe, kuma na yi masa irin duk abin da zan iya don ya yi bacci, amma abu ya gagara! ka yi masa wani dan kokari mana, ko ya samu ya yi bacci, ko dai ka yi masa abin da kaga ya fi dacewa, ni duk hannaye na sun gaji da daukar sa da jijjiga shi".
Sai ya ce da ita; "Saboda me kika rude haka? Dauki wannan littafin ki buda shi, ki ajiye a Gaban sa".
Sai matar ta fusata tana fada, tana cewa; "Yanzu wasa za ka yi mini game da wannan lamari"?,
Haka kuma za ka yi mini, bayan ka auro ni tun da kuruciya ta, ka gama biyan bukatar ka da ni, ka bar ni cikin yunwa da tsumma, alhali ina ta faman yi maka hidima ba-dare-ba-rana, kuma wannan yaro danka ne, ba agola ba?
Saboda me za ka Rinka wasa da hankalina a Kowane lokaci?"
Sai Shehu ya amsa mata da cewa; "Haba Hajiya? Ai kuwa ina yin bakin kokari na, wajen kyautata Rayuwar ki, saboda me za ki rinka yi mini irin Wannan magana mai zafi, kina tayar mini da Hankali"?.
Sai matar ta rage karfin muryarta, Sannan (afusace) taci gaba da cewa; To Wannan littafin na mene ne?, kuma wace fa’ida Za’a samu a cikin sa?
Sai ya ce: Kwantar da hankalin ki, wannan littafin “KADURI” ke nan, (Wani littafine, Mara ma’ana da ya kunshi Bayanai na rashin kan gado) Wanda duk lokacin dana karanta shi ga Almajirai a Masallaci, sai Bacci ya kwashe su, wasu ma har kiji suna Minshari".
To idan kuwa har zai iya sanya bacci Ya kwashe magidan ta masu gemu, kamar Wadan da aka yiwa sihiri saboda tasirin sa, Me zai hana ya sanya jariri ya yi bacci kamar ya Shaki banju?
Wani abun sai shehu
Hhhhh
JARABAWAR SHEHU JAHA
Wata rana a makaranta, sai malamin su Shehu ya shiga aji don yiwa su Shehu jarabawa, a cikin tambayar sai malamin ya tambayesu: “ka dauka kai soja ne da kuka dawo daga filin yaki, rubuta abubuwan da suka faru a lokacin kuna filin daga".
Lokacin da malamin ya fara tattara takardun dalibai, sai ya ga takardar Shehu bai rubuta komai ba.
Sai malamin yake tambayar sa "me yasa baka rubuta komai ba?".
Sai Shehu yace "ai tun a farkon yakin aka kashe ni”
Hhhhhhh
KOWA YA TAFI GA MAHAIFIYAR SHI
Wata rana hatsaniya ta hada Shehu da matarsa, sai matar ta fusata ta shiga daki ta fara tattara kayan ta a jaka.
Sai Shehu ya shigo ya same ta ya ce: “ina za ki je?”
Sai ta kalle shi a fusace ta ce: “gun mahaifiyata zan tafi”
Koda jin haka sai shima Shehu ya jawo jaka ya fara tattara kayan sa. Sai tace; “ina kuma za ka je?”
Sai ya ce: “nima gun mahaifiyata zan tafi”
Sai tace “toh idan ka tafi wa zai kula ma da yayanka guda shida da ke nan?”
Sai Shehu ya ce “ke zaki tafi ga mahaifiyarki, nima zan tafi ga mahaifiyata, suma sai su tafi ga mahaifiyar su!! kinga shikenan”.
Hhhhhh
INGANTACCEN LISSAFI
Wani mai kanti yana bin Shehu Jaha bashin kudi, sulai talatin da uku, sai ya zo wucewa ta wajen kantin mutumin nan, sai ya tsaya yace da shi “Dauko littafi ka nuna min kudin nan da kake bina in biya ka in huta” Mai kanti yaji dadi, ya dauko littafi yana dubawa, Shehu kuma yana lura dashi.
Sai Shehu yaga a shafin kusa da nasa Mai kanti yana bin limamin unguwar su kuma sulai ashirin da takwas, sai Shehu yace da Mai kanti “Nawa kake bina Ni?”
Mai kanti yace “Sulai talatin da uku”
Shehu yace: “To idan ka cire sulai
ashirin da takwas din Liman daga cikin sulai talatin da uku dake nawa, saura nawa kenan chanji?”
Maikanti yace “saura sulai biyar”
Shehu yace “To bani sulai biyar, kaga shikenan ba-kare bin- damo, tsakani na da kai babu sauran bashi”
Maikanti yayi murna yaga zai samu bashin da ya dade yana bi, nan da nan ya kawo sulai biyar ya bawa Shehu, Shehu kuwa yayi tafiyarsa.
Sai bayan da ya zauna ya nutsu, sai ya gano
lallai akwai kuskure a cikin lissafinnan, kuskure mai girma! Ya rasa kuma yanda zaiyi ya fita daga wannan gagarumin rikici da Shehu ya jefa shi.
Shehu gwanin lissalifi anya akwai wanda ya
kai shi iya lissafi kuwa??
Hhhhhhh
RASHIN LAFIYAR SHEHU
Shehu jaha yayi rashin lafiya aka kwantar dashi a asibiti, kasancewar sa mutun ne mai jama’a, yayi ta samun alheri daga wurin jama’a masu zuwa gaishe shi.
Sanadiyar haka da Shehu ya samu sauki, kullum in likita yayi niyyar sallamar sa sai yace “hum humm likita ni kawai nake jin abin da nake ji".
To daman gadaje hudu ne a jere, shehu shine a godo na uku.
To washe gari sai mai gadon farko ya mutu, washe gari na gefen sa ma ya mutu, washe gari daman shehu shine a gado na uku, ya zaga kama ruwa a ban daki ya dawo, sai ya tarar da na gado na hudu shima ya cika.
Sai Shehu yace "to layi take bi kenan,bata same ni bane shi yasa ta wuce, tunda ta kure layin to lallai zata dawo".
Nan take bai jira likita ba, ya tattare kayansa ya gudu
B*shakz
Ku kasance damu, domin samun wasu kayattatun hukayoyin.

Comments
Post a Comment