Musha dariya part 3

B shakz

 Musha dariya par 

3. 11- LABARIN LADO DA TANKO LADO yana zaune, a kusa da Abokin sa TANKO. 

 Sai LADO yace:- "Kai duniya ana abubuwan mamaki". 

 Sai TANKO yace:- "Me kuma ya faru"?

 Sai LADO yace:- "Wai ina zaune, Kusa da wata kwata, sai ga wata Mata mai ciki tazo zata tsallaka. 

 Sai naji dan cikin nata na cewa:- "Ina kwana Baba! Sai Matar nan ta lura, sai tace mun "kana kama da Baban sa shiya sa ya gaida kai". 

 Sai shima TANKO yace:- "Mhmmm!! Yo wannan har abun mamaki ne"? Nida aka yi ma abun da na kusa zaucewa" . 

Sai LADO yace:- "Wane abune"?

 Sai TANKO yace:- "Wai tun daga Kaduna, direban motar mu ya rasu, amma bamu sani ba, sai da muka zo Kano, Mun je gidan mai, anan aka tambaye shi "na nawa za'a zuba"?

 Sai aka ga ashe ma Direban ya rasu, harma ya tsandare!"

 Sai LADO Yace: "Wallahi karyane dan Ubanka"!!!


 12- LABARI BIRRAI MAI BAN DARIYA 

Wata rana birai suna zaune suna fira. sai wani karami, daga cikin biran yace: "mama, wai me yasa bamu da kyau, na gammu munana ne sosai har kunyan duba madubi nakeyi saboda munin mu".

 Sai uwar tayi murmushi tayi dariya sannan ta bude baki tace "jikana tsaya kaji, ai abin da yasa ka gammu munana, bamu da kyau kowa yafimu kyau, to sabo da mun yi kama da wanda yake karanta wannan LABARIN NE, da ace da wanda ya tura labarinne mukayi kama, to da zaka gammu kyawawa".

 13-ABARIN WANI BAZAZZAGE.

 Wani shakiyin Bazazzagi ne, ya yi dinkin sa babbar riga mai asake, akan wata dalleliyar shadda ruwan kwai. 

 Da ka ganshi, ka ga mai hannu da shuni. 

 Ai kuwa sai ya nufi gidan abinci (Restaurant), ya samu waje ya zauna, ya kwalawa mai kawo abinci kira, da karfi, ya ce: “Hado min plate na Naira 2,000, kuma ki hadawa kowa da ke wajen nan plate na Naira 3,000, sabo da idan ina cin abinci, ina so naga kowa yana ci”. 

 Duk mutanen da ke wajen suka fara godiya, yayin da mai restaurant ta zubawa kowa nasa, ta kawo masu hadin girma, Shinkafa, da dankalin turawa, da farfesun kayan ciki, ko kifi ko naman kai, ya dai danganta da abinda mutum ke so. 

 Kana ga hadin kwadon kayan lambu (da a turance a ke kira da salad).

 Bayan mutumin ya gama cin abinci, sai ya kuma cewa mai abincin “kawo min abin sha na Naira 500, kuma ki baiwa kowa na Naira 1,000 saboda idan ina shan abu, ina so naga kowa yana sha”. 

Mai Restaurant ta kaiwa kowa kayan shaye-shaye kala-kala, Nan fa mutanen wajen suka barke da shewar: “Allah ya kiyaye ka!”. 

 Bayan mutumin ya gama sai ya cewa mai Restaurant “kawo min resit na biya kudina, kuma ki kai wa kowa nasa resit ya biya kudinsa, saboda idan ina biyan kudina ina so naga kowa yana biya”. 

Yanzu haka mutumin yana kwance a asibiti, sabo da dan karen dukan da masu gidan abinci, da kuma mutanen da ya saka suka ci abincin da basu yi niyya ba suka yi masa.

 Yanzu haka ni kuma ina kwance, ina dariya, saboda idan ina dariya ina so na ga kowa na dariya. 

 14- LABARIN DAN FULANI ME SANIYA 

Wani dan fulani ne ya kai saniyar shi kasuwa zai siyar, amma ba’a siya ba. 

Sai ya dawo gida ransa a bace, Sai matar sa ta tambaye shi meyasa yake fishi? 

Sai yace mata: "ai saniya ce na kai ta kasuwa amma an ki siya".

 Sai matar tace "ai kai ne baka nemi shawara ta ba, gobe idan ka koma kasuwar kace saniyar tana da ciki". 

Haka kuwa akayi, dan fulani yakai saniya kasuwa yace: "tana da ciki"

 Nan da nan aka siye ta, tayi kudi fiye da kima. 

 kawai sai dan fulani yayi ta mamaki, yadawo gida yana murna. 

 Rannan sai akazo neman auren Diyar shi.

 sai aka kira liman ya yanke sadaki dubu 11,000, sai dan fulani yace "dakata malam nifa diyata tana da ciki, gwara ku sani dan likita ma yace yan biyu zata haifa".

 Hhhhhhhhhhh 


 15- SHEHU JAHA A GIDAN GIYA Kullum Shehu ya je gidan giya sai ya sha kwalba uku. 

 wata rana sai mai gidan giyan yake tambayarsa: "wai me ya sa kowa yana shan daya amma kai kana shan uku"? 

Sai Shehu ya ce: "ai mun yi alkawari ni da abokai na biyu, daya yana kasar Indiya, dayan kuma yana kasar Rasha, duk wanda zai sha giya sai ya sha wa dan uwansa". 

 A kwana a tashi, rannan sai ya zo ya sha kwalba biyu. 

 sai mai gidan giyan ya tambayi Shehu cewa: ”a cikin abokan nasa wanne ne ya mutu"? 

 Sai Shehu ya ce: "ba wanda ya mutu a cikin su, ni ne dai Allah ya shirye ni, tasu kawai nake sha, saboda girman alkawari". 

 Wai shin Shehu ya shiryu kuwa? 

 Ya kuke ganin wannan tuba na shehu


 16- MAKOCIN MU 

 Makocin mu Ne yakamu da rashin lafiya me tsanani, har takai ga ya kira boka domin yayi masa nagani.

 Abokin sa Yayi ta bashi hakuri, akan yabari har ALLAH ya bashi lafiya, amma mutuminka firrr ya ki, kawai sai yaja kyaleshi.

 Boka ya zo ya shigar dashi gidan sa, yagama tsubuce-tsubucen sa, sai yace masa: "ba zaka samu lafiyaba, amma za'a iya mayar da ciwon kan wani idan kana so "

 Shi kuwa ya yarda, boka yace: "toh yau mutum na farko dazai shigo gidanka yana shigowa kayi ihu kace 'Taaarh' "ciwon zai koma kansa, kuma zai mutu. 

sai dai fa Idan mutumin shima yace ""Retaarh " zai dawo maka da shi kai ka mutu". 

 Makocin mu ya yarda, boka yabar gidan da sauri, ya manta bai kar6i kudin aikinsa ba, sai da yayi nisa sai ya tuna. 

 Shi kuma makocinmu yadawo parlor, yazauna yana jiran wanda zai fara shigowa.

 Boka yadawo kar6an kudinsa, yana shigowa makocinmu yace: "Taaarh " 

Boka yayi ihun: "Retaarh " 

 Makocinmu ya kuma Ihun "Reretaarh "  
boka yace "Reretartaarh" 

 Yanzu haka tin jiya da safe suke ta faman ihu ji kake ""Rererererereretaaaaaarh....... Tahretahtahtahretaaaah.....

 An rasa ko waye zai hakura, daya ya mutu? 


 16-ABARIN WANI MAHAUKACI

 Wata rana GOBARA ta tashi a wasu shaguna, Jama’a suka yi ta kawo temakon gaggawa, da nufin dakile wannan wuta, dan kar tayi barna da yawa. 

 Amma duk da haka wutar tafi karfin su,sabo da mafi yawancin shagunan na sayar da KATIFU ne. 

 To acikin masu kashe wutar, akwai wani MAHAUKACI, wanda yafi kowa kokari wajen zubawa wutar RUWA, kuma shine yafi kowa ihun a kawo dauki.

 bayan gobarar ta gama qone shagunan nan tas, can sai akaji MAHAUKACIN nan yana cewa: “Amma fa wutar tayi Al-barka, ASHANA daya kacal na fa kyasta”. 

 Hhhhhhhh 


 17- KIN YIWA KAN KI
 Akwai wani mahaukaci yana bara a kasuwa, duk abin da ka bashi sadaka sai yace: "kayuwa kanka".

 Ashe akwai wata Mata, tana jin haushin wannan Kalmar da yake fada. 

Wata yana bara cikin kasuwar, sai matar nan ta kirashi, ta bashi sadakar abinci, Ashe ta saka guba (poison), ya karba yace: "kin yi wa kanki".

 Ya juya ya yi tafiyar sa, kawai sai Matar ta kwashe da dariya, tace: "daka yau! ba zaka sake cewa wani ya yiwa kansa ba" 

 Yaje inda ya ke zama, domin cin abin da ya samo daka bara, kawai sai ga wasu yara, sun taso daka makaranta. 

Suka ce da mahaukaci: "kayiwa kanka yau meka samo ne"?

 Yace: "ba kome sai wani abinci gashi kuci". 

 suka karba, suna murna, yace dasu: "Ku Kai kwanan cikin kasuwa"

 ai kuwa suna gamawa, daya daga cikin su yace: "wannan kwanun kamar Na maman mu".

 Suka ce "ehh shine".

 Ai kuwa suka nufi kasuwa, uwar Na ganin su da kwano tace: "a Ina kuka samu kwano"? 

 Suka ce: "Kin yiwa kanki ne ya bamu abinci mukaci". 

 18- LABARIN WASU SCIENCE STUDENTS SU UKU 

 Da dan BIOLOGY, da dan PHYSICS, da dan CHEMISTRY, su ka zo za su tsallake wani ruwa. 

 Sai suka tsaya, suna kallon ruwan, kawai sai sukaga wani katon kifi, yayi tsalle ya koma cikin ruwan.

 Sai wannan dan BIOLOGY yace: "yanxu kunsan a wane PHYLUM wannan kifin yake?" 

 Sai suka ce: "A'a".

 Sai yace: "bari na shiga na duba".

 Koda ya shiga, sai sukaji shiru-shiru, bai fito ba, Sai dan PHYSICS yace "qila WAVE ne yayi wani wajen dashi, bari na shiga na duba". 

 Shima da ya shiga shiru ba labari.

 Sai dan CHEMISTRY ya juya xai tafi, Sai wani Mutum yace masa: "kai ba xaka shiga kaga abinda yake faruwa ba"? Sai yace "A'ah ai ni na gama experiment dina, All of them are soluble in water. 


ZOMO NE 

Wani Sarkin ne, yakai ziyara gidan mahaukata, ya yita jawabi. 

 Bayan ya gama, sai shugaban tsaro na gidan, ya tattara su wuri daya, yace masu: "ko kun san wannan wanda ya yi jawabin"?. 

 Sai wani mahaukaci ya daga hannu, aka bashi dama, ya mike ya gama karewa sarki kallo, ga kunnuwan rawanin nan sunyi fiki-fiki, sai ya ce ai wannan ZOMO ne. 

 Hhhhhhhhh 


 19- LABARIN DAN SAKKWATO da INYYAMURI 

Dan sakkwato da inyamuri ne suke hira a kasuwa, DAN SAKKWATO: "abokina allah ya hada kawonan mu guri guda, duk daya muke".

 INYAMURI: "wazobia ne muke".

 DAN SAKKWATO: "kwarai da aniya". 

INYAMURI: "kuma Allah ya bamu albarkar kasa, ka gani a kudu muna noman, doya, coacoa, banana, rice, beans, milets, maize, granogth. 

DAN'SAKKWATO: " to in haka ne, mu a Arewa muna noman kare, da jaki, da shano, da akuya, Idan muka shuka daya sai mu girbe uku, ko hudu, ko biyar". 

 INYAMURI : Kai that one na miracle.

 20- LABARIN WANI MAI KWALEKWALE DA PROFESSOR.

 Prof ya zo wuccewa sai ya biyo hanyar da akwai ruwa, sai ya hau kwale-kwale. shike nan sai ya hau kwale-kwale.

 Ana tafiya sai prof yace da Me kwale-kwale: "ka yi karatu kuwa"?. 

 Me kwale-kwale Yace: "a.a" 

 Prof: "ka karanta sociology kuwa"?

 Me kwale-kwale yace "a,a"

 Prof: "psychology fa"? 

 Me kwale-kwale yace "a,a"

 Prof: "biology fa"?

 Me kwale-kwale Yace: "a,a" 

 Sai Prof yace: "ashe Kai jahili ne haka". 

Ashe me kwale-kwale yaji haushi, Amma sai ya boye, sai da akaje tsakiyan ruwa, sai yace: "Prof ka karanta bundumology"? 

 Prof yace "a,a"? 

 To "iyotology fa" 

 Prof yace "a,a" 

To "nisology fa" 

 Prof Yace "a,a" 

 Me kwale-kwale Yace: "yau zaka mutu jahili a ruwan nan himmm". 

Hahahahaha. 


 Da fatan kunyi nishadi, kun kuma dara. Mu hadu a part 4, in Allah ya yarda.

B*shakz

Comments