MUSHA DARIYA part 1
B shakz
MUSHA DARIYA!!!
1-LABARIN DAN FULANI DA NOKIA
Wani Dan fulani ne, ya siyi waya nokia 2700.
sai ya zo ya sami abokin sa, ya nanu masa, sai abokin nasa ya karbi wayar yahau google, yana browsing.
sai Dan Fulani yace: "nan kuma ina ne ka shiga"?
sai abokin yace: "google kenan duk abin da ka tambaya, zasu baka amsa, kuma har videos ma ana iya gani".
Dan Fulani yace: "to"
bayan kwana 2, sai Dan Fulani ya dawo gurin abokinsa, ya mika masa wayar, sai abokin yace: "lafiya JA'E" .
Dan Fulani: "yace yau ne google zaiyi aikinsa!, tambaya mun su wanne laifi kanwata kande tayima mijinta BELLO, har yayi mata duka sosai haka? idan ma da hali, har video ka samin nagani, dan naji dadin daukar fansa!!!!".
Hahaha abun dariya!
2-LABARIN SARKI ME BABBAN KOGI!!!
Awani 'kwauye, Anyi wani Sarki, yana da babban kogi mai muggan halittu.
wata rana, Sarki yasa Aka yi shela, cewa ana neman duk wani saurayi mai jini ajika, za'ayi wata Gasa, kuma duk wanda Ya cinye wannan gasar Sarki ya masa Alkawarin 'Yarshi, ko dukiya mai tsoka, Ko kuma a bashi Rabin Gari.
A katara dukka nin Jarumn Kauyen lzuwa Bakin wannan Babban kogin, bayan Anje, sarkin yace duk: "Wanda Ya shiga kogin nan, ya fito lafiya to zai samu kyauta mai tsoka".
Sarki bayan ya kammala jawabin sa, Aka bada dama afara gasa, amma abun mamaki!! ba wanda ya shiga, an kwashe kusan minti Ashirin ana jiran Wanda zai fara gasar anrasa.
Can! sai akaji wani Dan Fulani ya fada, Bunjumm!!! Sai jama'ar gari aka dautafi da lhu, Danfulani yayi kokari ya fito lzuwa bakin ga6a.
Bayan dan fulani yafito daga kogi, sarki yamar jinjina sosai, domun ya burge shi.
sai sarki yace masa: "Me kake bukata A guna na baka? Ka fadan komai kake so zan baka domun na jidadin Abunda kayi".
Sai Dan fulani Yace: ni abunda nake Bukata shine A gaya mun Dan lskan daya TURANI CIKIN KOGIN NAN!!!!!
Hahaha........
3-LABARIN MAHAUKACI MAI HIKIMA,
Wasu mutane ne ke cikin tafiya, a cikin motarsu a tsakiyar daji.
sai suka ji tayar motar ta gaba tana rawa, da suka tsaya, suka duba, sai suka ga ashe notocin dake daure da taya daya ta gaba, notokan ta uku sun kwance, sun fadi saura noti daya kawai
ke rike da ita.
Sun a ta shawarwarin abin yi don tsakiyar daji ne, ba gari a kusa, kuma ababen hawa basa wucewa, sannan waya ba zata yi rana a wajen ba.
Can!! sai ga wani mahaukaci zai wuce, sai ya kalle su, ya kalli tayar data kwance, sai ya kwashe da dariya har yana tuntsurawa kasa.
yana cewa "wallahi in nine sai in dauko daya a can, daya a nan, daya a can, sai in hada su uku in daure shegiya dasu,
habawa!!! sai tafiya hahaha wallahi wani aiki sai ni, su kuwa ba
za su iya ba"
sai ya kara tuntsurewa da
dariya
Duk mutanen nan basu kula da shi, ba ba sai mutum daya daga cikin su, wanda ya tsaya yake sauraren bankauran mahaukacin nan, sai yaga akwai hikima cikin zancen mahaukacin, sai ya fashe da dariya.
sauran abokan suka tambaye shi "me yasa shi dariya"
sai yace: "Ai kawai zancen mahaukacin nan za mu bi, mu kwanto notuna dai-dai, daga sauran tayoyin uku, sai mu daurawa wacce ta kwance,kawai muyi tafiyarmu lafiya lau ba matsala, don rashin noti dai-dai ba zai hana komai ba".
Sai sauran suka ce: "ya
akayi ya tuno wannan dabarar haka mu bamu tuno ba?
Sai ya nuna mahaukacin nan, yace kun ga mai hankalin da ya fahimtar damu, abin da bamu sani ba".
Duk sai duk kansu kowa ya cika da mamaki.
4- LABARIN SAURAYI DA BUDURWA
Wani saurayi ne, yaje zance.
sai budurwar sa ta nemi ya bata labari, sai yace: "to amma labarin part 1, 2, 3, da 4 me".
sai tace: "ya bata".
Saurayin ya fara kamar haka:-
Part 1: Wani mijine da matar sa, suna cikin tafiya a mota, can sai sun zo mararrabar hanya.
Sai yace wa matar: "wacce hanya zamu bi"?
Matar tace: "a'a dai megida! mubi hanyar da ta bi dama".
Ai kuwa! sai ya kwashe ta da mari, yace: "ni nake tuka motar ko kuwa ke? hanyar hagu za mubi".
Sai budurwar ta saka dariya, tace: "amma wannan miji akwai mugu".
Saurayi yace: "saura part 2, suka bi hanya, suna tafiya suka iso gun masu saida kifi, Megida ya siya musu.
Sai matar tace: "megida me za'ai dashi?"
Sai yace: "dafawa zakiyi".
Ai kuwa matar ta zabgeshi da mari!, tace: "kai kake girkin ko ni?? Soyawa zan yi".
Budurwar ta kyalkyale da dariya, tace: "amma ta burgeni, kaga sunyi duro".
Saurayi yace saura part 4.
sai budurwar tace: "a'a part 3 dai".
Ai kuwa sai saurayi ya kwasheta da mari! Yace "ni nake bada labarin ko ke"?
Hhhhhhhhh
Fatan kunji dadin kasancewa damu, kuma kunyi nisha.
Mu kasance musha dariys a part 2 domin samun labarai mask nishadantarwa.

Comments
Post a Comment