MU WASA KWAKWALWA

 B shakz

Wasa kwakwalwa


WASA KWAKWALWA 

1- Acikin sunayen mata, akwai wani suna me harafi 6.

ukun (3) farko sunan wani abu ne a yaren hausa, Kuma ko wanne mutum yana da shi.


Ukun karshe kuwa sunan wani abu ne, a yaren turanci, kuma ko wanne me gida in ya ganshi a gidan sa, tofa! sai ya kore shi, yake samun kwanciyar hankali.

Wanne suna ne?


WASA KWAKWALWA NA

 2- akwai wani abu, ana sai da shi a kasuwa.


Amma mai sayarwa baya so ya sayar, wanda ya siya ba shi zai yi anfani da shi ba,wanda zai yi anfani da shi baya ganin sa.

 wannan wane abu ne ???


WASA KWA-KWALWA NA

3- Wane abu ne Fari kamar Ruwa, kuma baki kamar tukunya, Namij ya na amfani da shi sau uku a rana, Mace ta na amfani da shi sau 1 tak! a Rayuwarta.

 An fade shi a Alkur'ani, a Larabci ya na da harafi 3, a Hausa kuwa 4.

Mene ne wannan ?



WASA KWAKWALWA NA

 4- wani yaro ne aka tambaye shi, cewa shekarun sa nawa, sai yace bai sani ba.

amma yasan cewa; shekarun sa rabin na maman shi ne, amma kuma bai san shekarun maman tasa ba.


amma tsakanin shekarun ta da na baban shi tsakanin su shekara 7 ne, kuma bai san shekarun baban nasa ba shima.


amma yasan cewa; da shekarun sa, da na mamar sa, da na baban sa, in an tara su shekara 100 ne.

A.nawa ne shekarun yaron ? 

B- nawa ne shekarun  mamar sa ?

C-nawa ne na baban sa ?


.

WASA KWAKWALWA NA 

5- Da akwai wata karamar hukuma, a birnin kanon dabo, Karamar hukumar tana dauke da harafai guda 8.


-Idan ka cire harafai 2 na qarshe, zai baka sunan wani abu, wanda dukkan mutane suna alfahari da shi.


--Idan ka cire harafai 4 Na farko, zai baka sunan wata aba, wacce duk mutumin da aka ga yana yi, ana cewa mutum bashi da kunya.


-Idan kuma ka cire harafai 2 na farko, dana qarshe, zai baka sunan wani abu, wanda idan aka yiwa mutum dole sai yayi jinya.


-Idan kuma ka cire harafai 4  na tsakiya, zai baka wata kalma, wadda dole sai da ita ciniki yake kulluwa.

Wacce karamar hukuma ve wannan?

Wayanne abubuwa ne wayannan?



6-Wane abune Tunda aka haife ka aka hada ka da shi? amma ba da shi aka haife ka ba.



WASA KWAKWALWA NA

 7 -akwai wani abu, idan yana baki yanada tsafta, amma idan yayi fari kuma to yayi Datti?

menene wannan abun?

 

WASA KWAKWALWA NA

 8- Wasu abubuwa ne 'yan'uwa guda biyar.

 Uku suna a inuwa, biyu suna a Rana.

Kuma har abada ukun nan suna a inuwa, basa zuwa rana, haka Kuma biyun nan, basa zuwa inuwa.

to wadanne abubuwa ne?



WASA KWAKWAKWA NA

 9- Wane abu ne ana cin sa kafin a dafa, amma idan an dafa ya lalace? 


kuma Maza na chin sa, Mata na cin sa, Sanna yafi komi arha a Nigeria, ayi ta ci har safe baya karewa.

wannan abun miye shi??? 🤔🤔


WASA KWAKWALWA NA

10- akwai abunda namiji yake yi so biyar a rana, macce kuma so biyu.

To menene shi?


WASA KWAKWALWA NA 11- ️Wanne Abune Naka, Amma Wadanda Suka san ka Sun fi ka Anfana Da shi ?

Me nene shi?🤣



WASA KWAKWALWA NA

 12- Wasu mutum biyu ne su kai fada, su ka kashe kan su.

da aka zo sai aka tarar, daya ancire masa hannaye.

daya kuma ansare masa kai.

idan kaine alkali a tunanin ka, waye yafara kashe wani?


WASA KWAKWALWA NA 

13- da ace jiya zata kasance gobe, da yau tazama asabar.

Wacce ranace wannan?


WASA KWAKWALWA NA

 14- Wanne abune kullum idan aka bashi abinci, yana ci, Amma idan aka bashi ruwa zai mutu??

Me wanna??


WASA KWAKWALW NA 

15- Wani abu ne, mata suna sonsa, maza suna tsoronsa, yara na wasa dashi, sarakuna na kyauta dashi.

Menene wannan??



WASA KWAKWALWA NA

 16- Akwai wani abu yana tafiya tsawan shekara 15, amma kai a 5mn zaka wuce shi.

Wannan wanna irin Abu ne??



WASA KWAKWALWA NA 

17- Kwai wani abu asalin sa ja ne, amma idan ya mutu dakan sa yana komawa fari, idan kashe shi aka yi, yana komawa baki?

Wanne abu ne wannan


WASA KWAKWALWA NA 

18- 50-0+40×0×0+1×0

A1

B91

C50

D51


Wannene amsar?


18- gwada cire sunaye uku, kacal! acikin sunan wannan kasar ITALIYA.


Mun gode da bibiyar mu, da fatan kunji dadin wasa kwakwalwar.

Comments

Popular Posts