Hikayar laila da majnun
HIKAYAR LAILA DA
MAJNUN
B* shakz Hikayoyi B*shak
Da sunan Allah me rahma me jin kai.
Allah shi ne Sarki mafi daukaka daga dukkan sarakuna, Shi ne mafi tsarki daga dukkan abubuwa, Tsira da aminci su tabbata ga Manzon sa kuma Annabin sa, Muhammadu dan Amina
(SAW).
Hikayar Laila da Majnun an ba da ita kimanin shekaru dubu da suka wuce, kuma an bayar da ita ta fuskoki da dama, amma dukkan fuskokin sun hadu
akan tushe daya, watau tsarkakkiyar soyayya ce tsakanin su.
Ga irin hikayar da muka rairayo:
Wani saurayi mai suna Qays ibn Mulawwah dan kabilar Banu Amar.
Qays ya kasance mai fasaha, da basira a makarantarsu, sai dai ya kamu da soyayyar Laila bint Mahdi Ibn Sa’ad, an fi kiran ta da Laila Amiriya.
A hankali ya rika nuna mata soyayya ta hanyar kulawa da sauran alamu, Duk lokacin da ta makara zuwa makaranta, sai hankalin sa ya tashi ya rasa sukuni, gaba daya sai ya zuba wa kofa ido, ba ya mayar da hankali ga karatun sa.
Wata rana da zuciyar sa ta cika da bege, ya ji kirjin sa kamar ya fashe, bai san lokacin da ya rika rubuta sunan Laila a takardar rubutunsa ba, maimakon abin da ake koya musu.
Dalibai da suka ga haka sai suka hakikance lallai ya yi nisa wajen kaunar ta, Da haka ita ma Laila ta soma kaunarsa, ya zamana duk makarantar
an san su a matsayin masoya.
Shi Qays kamar tun yana yaro k’arami masu ilmin taurari suka bayyanawa mahaifin sa cewa; zai kasance wanda rayuwarsa za ta fada cikin wahala da musiba.
Suka kara da cewa; idan ba
a yi da gaske ba ma zai iya haukacewa.
Tun daga wannan lokacin mahaifin sa ke samo masa lak’ani da magunguna da addu’oi, Yayin da ya data sai
mahaifin sa ya dauke shi ya kai shi Dimashka karatu, inda anan ne ya hadu da Laila.
Ita Laila ta kasance ‘yar shugaban kabilar Sharwaris, wadda a da zamanin Jahiliyya ba sa ga maciji da kabilar su Qays.
Laila da Qays suka zama tamkar jini daya tsoka, idan daya bai ga daya ba sai ya kama rashin lafiya, amma Qays
abin na sa ya fi tsanani, domin kuwa har wakoki yake rubutawa masoyiyar sa, yana karanta su a ko’ina.
Daya daga wakokin da yayi mata ita ce:
Na so ki ya mai kyau dan gaske.
kece wata ko tauraro mai haske.
Kin shiga ruhi na, kin mammallake, In babu ke, to ni kuwa na tabbatar ba zan rayu a duniyar nan ba.
A makaranta aka rinka gulmar su, ana nuna Majnun duk inda ya wuce, sai ya kasance idan ka yi masa abu ka ce masa; ya yi hakuri don Laila, shikenan zancen ya wuce.
Da dalibai suka gano lagonsa, suka rika dauke masa kayan rubutu, suna cewa; ya basu domin darajar Laila, ba musu sai ya ba su.
Maubin (malamin) makarantar ya damu
kwarai da irin wannan al’amari, musamman da ya ga Qays yanzu sunan sa ya bace, ya koma Majnun Laila (Mahaukacin Laila).
Sai malamin ya rubutawa iyayen su takarda yana fadakar da su halin da ‘ya’yansu ke ciki.
Iyayen Laila suka cire ta daga makarantar, aka kirawo wani kwararren malami yana koya mata karatu a gida.
Ciwon so ba shi da magani! Maimakon hakan ya yi magani sai ya dada rikita al’amari.
Majnun ya daina karanta komai, kullum sai kuka sai waka, duk abinda ya gani sai ya ga yana masa gizo da kamannin Laila, Nan da nan sai ya fara rera wa abun wakar so.
Mahaifin Majnun ya zo takanas ya daukeshi zuwa wajen likitoci, da ‘yan tsibbu, da bokaye, da sauran masu da'awar magani, duk abin ya zama tamkar wutar kara ake ayayyafawa
fetur.
Abokai da ‘yan uwa na kusa da na nesa suka zo, domin tausasa zuciyar Majnun ya daina tunanin Laila, amma duk a banza.
Wani daga baffanin sa ya ce masa, “wai kai Qays me ka gani a jikin Laila, da ka nace mata haka"?
Ka zo mu je na nuna maka mata dubu wadanda suka fita kyau, da kyan fasali, da asali, da mulki da dukiya, da sarauta, ka zabi wadda tayi maka.”
Majnun ya dube shi ya girgiza kai ya ce; “idanun Majnun Qays ba wanda suke so da gani tamkar Laila.”
Ya daga hannu sama ya ce; “Ya Allah! Na san ba ka yi kyakkyawa a duniya
tamkar Laila ba, Na tabbata ita tana daga asalin Hurul Aini da suka zo
duniya shan iska, Ya Allah alk'awarin ka baya tashi, na tabbata daga kan Laila ba zaka sake wata kyakkyawa ba Ya Allah ka ba ni Laila!”
Wani daga kabilar su ya ba shi shawarar ya dauki Majnun zuwa Makka, ya roki Allah a ka’aba, kan Allah ya dauke masa son Laila a zuciyarsa.
Amma saboda tsananin soyayya, a yayin da suka je dakin ka’aba sai mahaifin sa yace masa; "kama tufafin ka’aba, ka roki Allah ya cire maka son Laila".
sai Majnun ya kama yace; “Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Laila ba"
Ya k’ara da cewa, “ Ko Luqman, babban malami kuma masani, na tabbata ba shi da maganin ciwon so, Idan ma yana da shi ina fata babu wanda ke tsakani na da Laila"
Sai Ya raira wadannan baitoci a Makka;
"na ce da shehin malami, Wai shin wace ke cutar da ni? Shin lefi take yi, to a sanar da ni.
Shehi ya ce “dana bi a hankali, azaba zata je can gare ta.
Na yi farat na ce masa “a’a na yafe, da azaba ta samu Laila ko a gefe, ba ni kauna gwara ta same ni a lafe.
Da na daina sonta a barci ko farke, gwara na mutu da ciwon kaunar ta".
Sannan ya ce da murya mai raurawa;“Allah ka bani lailaa!".
Yayin da iyayen Majnun suka ga haka. kullum lamarin nasa k’ara lalacewa ya ke yi, sai suka ga babu mafita face su je su nemi auren Laila wurin iyayenta.
Wannan shine mataki na karshe, da suke ganin zai magance matsalar dansu.
Suka tashi jakadu na musamman zuwa garin su Laila, suka bayyana musu irin halin da d’ansu yake ciki game da soyayyar Laila.
Sannan jakadun suka nemi aurenta a madadin sa.
Iyayen Laila suka amsa da cewa, “mu a wajenmu abin da Majnun yake yi domin ‘yar mu wulak’anci ne mai girma ga 'yar mu, Kuma duk da yake mun san cewa Laila tana da ra’ayinsa, amma ba zamu iya aurar da ita gare shi ba, A dalilinsa mun cire ta daga makaranta, mu a wajen mu mahaukaci ne kad’ai zai rik’a irin abinda Majnun ke yi.”
Dan haka iyayen Majnun suka ji dadi, tunda su a tsammanin su idan har ya daina shiririta da yake yi akan laila, iyayen Laila za su amince, su aura masa ita.
Saboda haka suka shiga tausasar, sa suna ba shi shawarar ya nutsu, ya daina abubuwan da yake.
Majnun ya amince da haka, amma da sharadin za a kai shi ya ga abar kaunar sa Laila.
Suka shirya suka tafi tare da wakilan sa zuwa garin su Laila, Aka sauke su a wani babban gida, sannan aka kawo musu abin ci da abin sha, An kawata wajen da fitilu masu launi iri dabam-dabam, Sannan an kunna turaren wuta, ko ina sai kamshi ke tashi, An jera kasake masu yawa cike da abinci, da fulawoyi masu k'ayatarwa.
Zuciyar Majnun kuwa ta kasa nutsuwa, ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya tafi ga masoyiyarsa, Bai iya jurewa ba sai ya mike a gaban waliyan Laila ya rika safa da marwa, yana rera wadannan baitoci;
"Na yi nisan zango don na gane ki, Ga shi na zo nan ina ta neman ki, Ina kike ina kika shiga ne in ganki, Zuciya ta tana ta jidali domin nemanki, Ya ki taho abar begena, don Allah nunan kanki".
Jimawa kad'an sai ga karen da Laila take zuwa da shi makaranta ya shigo gidan, Majnun sai ya ji ya kasa jurewa, ya zabura wajen karen nan ya rungume shi yana sumbatar sa yana cewa; "Na ga rabin Laila saura rabin, ya wanan karen mai baiwa, yi maza je ka ingizo min Laila."
Garin wutsulniyar da kare yake yi da kafafu ya ture farantan abincin, suka bata gaban rigar wani dattijo mai fada aji a dangin Laila.
Shi kuwa gogan naka sai ya dauki wani tsiron fulawa ya makalawa karen a wuya yana ce masa; "maza je ka kaiwa Laila ka mika min gaisuwa ta gare ta."
Duk jama'ar wurin suka yi tsit suna kallon ikon Allah, wakilan da suka rako shi suka rasa inda zasu sa kansu domin kunya, Wakilan Laila kuwa suka cika da fushi iyakar fushi, Wani daga cikin su ya fusata ya ce wa Majnun, "Shin bautar kare ka zo ko kuwa maganar aure?"
Kai tsaye Majnun ya kalli mutumin ya ce; "wannan karen a wuri na ya fi mutum dubu daraja, domin a jikin sa ina ganin surar masoyiya ta, wadda kaunar ta ke tare a zuciyata dare da rana."
Duk wuri aka dauki salati, Jama'a suka rika zunden sa, suna cewa ya haukace.
Dattijon nan da aka batawa riga da abinci ya mike a fusace, ya fice daga gidan, duk jama'a ma suka watse.
Wannan jama'a suka rika rantsewa, cewa haukan nan dai bai rabu da shi ba, sai ma abin da ya yi gaba.
Daga nan iyayen Laila suka fito kai tsaye suka ce ba zasu aurar da 'yar su ga Majnun (mahaukaci) ba.
To daga nan sai duk wani fatan samun nutsuwar sa ya zama akin banza, suka tabbatar ba za su iya magance masa matsalar ba.
don haka suka sa masa albarka suka kyale shi bisa halinsa.
Shi kuwa duk inda ya shiga, lungu da sako, sai ya rika cigiyar Laila ko sun san inda take, da yadda zai hadu da ita.
A haka har ya yi kicibis da wani jakada, mai aikin raba takardu gari-gari, Ya tambaye shi labarin Laila, Jakada ya ce masa; "Laila da iyayenta sun tashi daga garinsu, sun koma wani gari mai nisa, daga nan garin zuwa can tafiyar mil dari da ashirin ne".
Majnun ya shiga yi masa magiyar; zai ba shi sako zuwa ga laila, Jakada ya amince zai karb'i sakon takarda kurum babu wani abu.
Majnun ya zauna yayi ta rubutun shafuka da yawa, har jakada ya gaji ya ce masa, "wacce irin wasika ce haka?"
Majnun ya ce, "wasikar soyayya ce bata da karshe."
Jakada ya yi dariya sannan ya ce, "to samu waje ka diga aya, ka bani na tafi"
Majnun ya nade takardar ya ba shi, Sannan ya nemi yana so ya yi masa rakiya kadan, Suna tafe Majnun na ba wa jakada labarin abar k'aunarsa Laila, shi kuma yana ta mamaki.
Sai da suka shafe mil goma, Majnun na tafiya a kasa Jakada na bisa rak'umi.
Jakada ya ce masa; "to ka koma haka, ka yi nisa kwarai da gidan ku."
Majnun ya juyo ya fara tafiya, sai kuma ya juya ya ce da Jakada da babbar murya, "ya kai kaunataccen abokina! Wallahi na yi mantuwar wani muhimmin sako da nake so na rubuta mata!"
Jakada ya ce, "to gaskiya ba zan tsaya ba, sai dai ka fada min da baki na fad'a mata".
Majnun ya dowa ya same shi suka rankaya, Suna tafe yana fada masa sakon, har suka share wasu mil goman.
Jakada ya ce, "ka koma haka kada a neme ka a gidanku."
Ya kara juyowa ya fara tafiya, sannan ya waigo ya ce, "wallahi ba domin kada ka ce na matsa maka ba, da na k'ara maka wani sak'on, Muhimmi ne kwarai na mance da shi".
Jakada ya ce, "to matso ka fad'a min!"
Suka sake rankayawa yana ta fada masa sako, Haka suka yi ta yi har kafin su ankara sai ga su a garin da Laila take.
Jakada yayi mamakin irin wannan soyayya, sannan ya ce da Majnun, "Babu bukatar na kai wa Laila sako, domin ga shi mun zo garin da take."
Da jin haka Majnun ya cika da farin ciki da murna, Ya fadi sumamme, don tsananin farin ciki.
Bayan ya farfado jakada ya ce masa; “bana so a ganka, domin jama’a na iya kama ka, su yi maka wulakanci, kafin ka ga Laila.
Ga wani kango can ka shiga, ka zauna a ciki, ka huta, domin ka yi tafiya mai yawa, Zan isar da sakon ka ga Laila yanzun nan.”
Majnun ya yarda da shawarar jakada, ya shiga kangon nan ya zauna, zuciyar sa na harbawa kamar ta tsage.
Sakamakon tafiyar da ya sha, duk yayi
futu– futu, Tufafin sa sun yi jawur da kura, gashin kansa duk ya kukkulle, ga
kafafun sa sun yi fato– fato da kura, da faso, da kaushi. Ga shi nan dai!! yarbajila da shi.
Duk da haka, da ya tuna cewar yana garin da Laila ta ke, gaba daya sai ya ji ran sa ya yi fari fat, Ya cika da murna da farin ciki, zuciyar sa ta cika da bege, ya rika rera waka yana cewa;
"Na aika sako na wajen masoyiya ta, Zuciya ta da rayuka na gaba daya, na mika su wajen ki, gimbiya, ke ce tawa, hakika na fadi gaskiya, Na sallama miki kai na lahira da duniya"
Daga nan sai gajiya ta kama shi, ya ji yana so ya kwanta, To amma sai ya rika tunanin; shin a wanne bangare Laila take???
Domin baya so ya kwanta inda kafar sa zata rika kallon wajan da take, domin a wajen sa hakan cin amanar kauna ne, zai iya shurin ta bai sani ba.
Ya tsaya yana tunani, shin tana gabas ne, ko yamma, ko kudu, ko kuwa arewa?
Duk inda ya sa kansa, sai ya tuna kila a
wannan bangaren take, sai yayi maza ya sake waje.
Daga baya dai sai ya samo igiya, ya daura a kafar sa ya samu gini ya daura kafar, yana zamana kansa yana kasa, kafarsa a sama, yana reto kamar jemage.
A wannan yanayi kuma bai fasa rera mata wak'a ba yana cewa:
Hajjina da Umarata na wajenki, makka ta da Madina sune garin ki, Baitil Mukdis a wurina shine murmushin ki, Arzikina duk ni dai in ga dariyarki, Na sallama kaina gaba daya wurinki"
kishi ruwa na damun sa amma babu ruwa a kurkusa, haka ya hakura wutar bege na hura shi, tana kone masa sassan jiki da zuciya.
Jakada ya yi sallama a kofar gidan su Laila, laila ta fito, ya ce mata, "na yi kokari da gaske domin na yi miki magana, game da masoyinki Majnun, wanda ban taba ganin tamkarsa ba, a fagen so."
Ya kwashe labarin duk yadda suka yi ya fada mata, sannan ya kara da cewa, "yanzu haka nabar shi a bayan gari, domin gudun kada awulakanta shi, idan
jama'a suka ganshi."
Da Laila ta ji haka sai tausayinsa ya kama ta, ta tafi wajen uwar goyon ta, ta ce mata; me yake faruwa ga mutumin daya yi tafiyar mil dari da ashirin a kasa, ba tare da ya huta ba?"
Tsohuwa ta ce, "wannan mutumin ba
zai rayu ba mutuwa zai yi."
Laila na jin haka sai ta ji ta shiga damuwa, ta sake ce mata, "babu wani magani"?
Sai tace "Magani daya ne a sanina, Dole ya sha ruwan saman da aka ajiye shi, akalla shekara daya, kuma dole ruwan ya zamana maciji ya sha shi, Sannan ya daura igiya a kafar sa, ya zamana kansa na kallon kasa, zuwa wani lokaci, Idan ya aikata hakan watakila zai tsira da ransa."
Da ta ji haka, sai ta yi tagumi, tana cewa, "wannan magani akwai wahalar samu, kai ba ma zai yiwu ba."
Ta daga hannu sama, tana
rokon Allah ta ce, "Ya Allah mai kulla soyayya, mai bayarwa mai hanawa, ka
taimaki Qays Majnun ya samu wannan
magani".
Ta shafa, sannan ta yi ajiyar zuciya, ta ce, "soyayya bata da magani sai ita
kanta".
Allah da ikon sa, Majnun na rataye da kafar sa a sama ga kishirwa na addabar sa sai ya kwance igiyar ya tafi neman ruwa, bai samu ruwa ba, sai wani tsohon kasko a wani lungu, Ya tarar wani zabgegen maciji na shan ruwan.
Ya kore shi, sannan ya kafa kai ya shanye ruwan gaba daya, Ya samu waje ya zauna yana wake-waken sa.
Da gari ya waye, Laila ta shirya abinci mai rai da lafiya ta kirawo kuyanga a boye, ta fada mata komai, sannan ta nemi ta kai wa Majnun abincin inda yake a bayan gari, Kuma ta bata sakon a fada
masa cewar; ita ma tana nan tana kaunarsa kuma tana son ganin sa, amma da zarar ta samu dama zata zo ta ganshi.
Yayin da kuyanga ta je wajen, sai ta tarar da mutane biyu, daya ya hada kai da gwiwa kuma duk ya rame, ga kansa nan
duguzunzum, dayan kuma mai kiba jawur da shi, sai dai ya manyanta.
Kuyangar ta dube su duka biyun, ta ga babu wanda ya cancanci Laila ta so shi. Ita kanta ma ta ji duk basu kwanta mata a rai ba, balle kuma Laila.
Duk da haka domin cika umarni sai ta ce, "a cikinku waye Majnun? Mai kibar ne kadai ya ji, sai ya taso wajenta, ya ce; "me ya faru?"
Sai ta nuna kwandon abinci ta ce, "cewa aka yi na kawo masa wannan daga Laila."
Nan da nan ya karbe abincin, yana cewa; "ni ne Majnun.
Ta fada masa sakon Laila, ya yi mata dan wasa haka, sannan ya sa abinci a gaba ya cinye, Ya ragewa Majnun dan kadan, daga wannan rana kullum sai ta kawo masa abinci da sakon baka, shi kuma sai ya cinye ya rage kadan domin Majnun.
Kullum Laila kan tambayi kuyanga, "me ya ce ki fada".
Ta dubi kuyanga ta ce; "su nawa ne a wurin?".
Kuyanga ta ce; "su biyu ne".
Laila ta yi ajiyar zuciya ta ce, "to yau ba
za a kai abinci ba, amma zan sa ki musu wata jarrabawa, domin mu gane,Majnun na gaskiya."
Ta bata wuka ta fada mata abin da zata yi da ita, Kuyanga ta tafi wajensu Majnun, ta tarar da jakada na tsaye yana jiranta.
Tana zuwa ya soma yi mata sannu da zuwa. Ya mika hannu da nufin ya karbi gara, maimako haka sai ya ga ta fito da wata sharbebiyar wuka!, Ta ce, "Laila bata da lafiya, ana bukatar jinin masoyin ta kwalba daya, wanda da shi za a hada maganin, shi yasa na zo wajen ka na diba."
Yana ganin haka, sai jikin sa ya kama rawa, ya ce; "to ni dai ba masoyin ta bane, kuma ba ni ne Majnun ba, gashi can a zaune."
Ta wuce zuwa wajen Majnun, ta fada masa kamar yadda ta fada wa Jakada.
Yana jin haka ya karbi wukar da hanzari, ya sumbace ta sannan ya ce; "na gode wa Allah da ya kaddara cewa jini na ne zai warkar da ciwon masoyiya ta."
Ya dirza wukar a hannunsa, Maimakon jini ya zubo, sai wajen kurum ya yai farat fat, alamar babu jini, Ya sake keta wani wajen, nan ma babu jinin, sabo da bai ci
abinci ba ballantana a samu abin da ake bukata.
Da ya ga haka, sai ya soka wukar a hamatarsa, inda babbar jijiyar jini take, nan jinin ya rika kwarara, ya tara, ya mikawa kuyangar, wadda tuni tsoro da mamaki sun hana ta motsi.
Yayin da ta koma gida, ta shaida wa Laila irin abin mamakin da ta gani wajen Majnun, sai Laila ta yi ta kuka tana tausaya masa.
A cikin gari kuwa, labarin Majnun ya cika gari, sai aka samu wasu shakiyan matasa suka dauko kulake suka nufi inda yake, Tun daga nesa da Jakada ya hango su, sai ya hau taguwar sa ya sulale, ya bar Majnun yana wake-waken sa, yadda ya saba.
Matasan na zuwa suka hau bugun sa, suna shuri da naushi da yakushi, Suka daure shi da igiya, sannan suka tsaya daga nesa suna jifarsa.
Da Laila ta ji labari, sai ta sheko da gudu, ta zo ta kare shi daga bugun mutane, ta rika zagin su, tana korarsu.
Shi kuwa duk da yana daure ga bugu da ya sha, amma sai ya ji ransa ya yi fari fat da ganin abar begen sa, ya rika ambaton sunan ta yana cewa;
"Laila, Laila, Laila tawa ce, domin akan ki ne na haukace, wasu na kallona wai na karkace, to amma fa yau na samu dace, da ganin haskenki ya masoyiya"
Iyayen Laila suka turo aka tafi da ita
gida, tana kuka, da suka ga lamarin ya
wuce sanin su, sai suka yi shirin yin balaguro nawani lokacin.
Domin a tsammanin su idan suka tafi, suka jima Majnun zai gaji da neman ta, har ya saduda ya hakura.
Suka shirya kaya, suka tafi wani gari, da basu ambata ba, gudun kada ya ji ya bi su can.
To amma kafin su tashi, Laila ta rubuta takarda a boye, ta ba wa kuyangar ta ta
kaiwa Majnun.
Ya bude ya karanta cewar; "Masoyina, bulaguro za mu yi wani gari mai nisa, haduwar mu zata yi wuya anan, idan zaka iya mu hadu a zangon farko cikin sahara".
Yana gama karantawa ya ce da kuyangar, "ki gaishe ta da kyau da kyau, kuma ki fada mata cewar ina nan tafe."
Lokacin da su Laila suka sauka a zangon farko, sai ta tafi ita da kuyangar ta, zuwa inda ta ce masa ya je zata same shi.
A tsammanin ta bai isa ya zo wurin ba, a wannan lokacin, domin su a abin hawa suke, shi kuwa a kasa yake, tana zuwa ta
same shi ya hada kai da gwiwa, yana ta kiran sunanta, "Laila! Ya Laila!! Ya Laila!!!"
Ta karaso wurin sa tana mai cewa,
"Ya Majnunun Soyayya ga
Lailar ka ta iso"!!l
duwatsun kusa da na nesa suka dauki muryarta tana amo, Nan da nan yazabura zuwa gare ta, yana mai cewa,"shin da gaske ne, Laila ke ce anan?"
Ta amsa "ni ce!"
Ya mika mata hannu ta rike, sai suka ji
kururuwar mahaifan ta suna neman ta, domin a cigaba da tafiya.
Ta juya da hanzari, ya ce; "Haba Laila kada ki tafi ki bar ni da begen ki!"
Ta ce, "kar ka damu, idan na dawo za mu hadu anan".
Yace "yaushe za ki dawo?"
Ta ce, "ban san lokacin ba, amma da zarar mun taho zan aika maka."
Da haka ta tafi, ta bar shi anan, Majnun ya ce a ransa, "idan ta dawo wa zata aika ya fada min? A ina dan sakon zai same ni? Kawai bari na zauna anan din har sai ta dawo."
Ya share wuri ya zauna, ba shi da wani abinci sai ganyen bishiyar da ke wajen, yana shan ruwa dake bubbugowa karkashin dutse.
A kullum zancen sa shine; kiran sunan Laila, da addu'ar ta dawo ta same shi, A haka har tsiron bishiya ya fito daga 'ya'yan itacen da yake jefarwa, ganyen ta ya nannade masa jiki, ya zama tamkar bishiyar a jikinsa ta tsiro.
A can garin da su iyayen Laila suka je da ita kuwa, sai wani attajiri ya fito yana sonta da aure.
Nan take ya bawa iyayen rakumma dari,
gami da wasu kyautuka masu yawa.
Da Laila ta ga alamar lalai za a aurar da ita gare shi, sai ciwo ya kama ta, Ta yi ta fama, iyayen suka yi nufin komawa gida,
domin magani, in yaso idan ta warware sai a yi auren.
A hanyar su ta dawowa suka sauka a wannan zangon, Duk da tana fama da jinya, Laila ta taso zuwa wurin da suka yi alkawari da Majnun.
Ta kusa isa kenan ta gamu da wani mutum ya ce mata; "yarinya kada ki je wurin nan da kika nufa, Akwai wata fatalwa mai kamar bishiya da ta bayyana, Kullum tana kiran sunan Laila, Laila".
Da ta ji haka, sai ta tabbatar Majnun ne bai tafi ba, Ta karasa wurin da gudu.
Yana ganinta, yayi zumbur ya mike tsaye yana mai farin ciki, yana cewa "Laila kin cika alkawari? Laila ke ce kuwa? Laila za ki aure ni??"
.
Kasancewar ya jima sosai a zaune baya mikewa sai jiri ya debe shi, a lokaci guda
kuma zuciyar sa ta buga, sabo da tsanannin farin ciki, Kan sa ya gwaru da dutse ya fadi matacce.
Laila na ganin irin wannan sadaukarwa, ta kasa hakurcewa, zuciyarta ta raurawa, kirjin ta ya yi matukar kunci, Nan take numfashin ta ya dauke ta fadi a wajen matacciya, Bayan wasu lokuta aka iske gawarwakin su, sai aka binne su kusa da kusa.
Karshe kabarin Majnun ya tsuro da bishiya, kabarin Laila ya tsuro da bishiya, bishiyoyin suka hade.
A yanzu haka! masoyan kwarai na kai ziyara wajen kabarin Laila da Majnun.
.
WANAN SHINE KARSHEN KARSHEN LABARIN WANNAN SOYAYYAH
B*shakz
Ku kasan ce damu, don samun wasu hikayoyin masu kayatarwa.

Comments
Post a Comment