HIKIMAR RAYUWA A KALAMAI NA HIKIMA




 HIKIMAR RAYUWA A KALAMAN HIKIMA



    ~1-"Mai hikima zai iya koya daga tambayar wauta, "Fiye da yadda "Wawa ke iya koyo daga amsar Mai hikima. "



        ~ 2-Ba kowane mutum ne yake da azancin tsara magana kuma mutane su fahimta cikin sauki ba.

Amma kai ma da Allah Ya ba ka hikimar zayyana zance, ba kawai ya ba ka ba ne don ka kece raini ko tsere sa'a ko ka  nemi kudi ko kuma don a kira ka shegen-kano.

Ka nutsu, ka san hanyar da za kai amfani da hikimarka. Domin Ubangijinka zai tambaye ka a kan kowace ni'ima da ya yi ma.



      ~3-"Lokacin da mutane ke alfahari da maganganunsu, Ku yi alfahari da shirun ku. "In ji Luqman 

    


      ~4-Ita fa hikimar zance, ba yawan surutu kesa a iya ta ba!!.



      ~5-Yawan surutu alamar tabuwar hankali ne.



     ~ 6-Ba kowace magana ce ake ba da amsar ta ba, ko shiru magana ce.



      ~7-Ana yin danasani ne a kan magana, amma ba'a yi a kan kawaici. Ka kama bakin ka, kar kayi magana mara anfani.



      ~8-Kada ka dauka cewa; duk wanda ya yi shiru kurma ne.

Wani ya yi shiru ne yana jiran lokaci.

wani ya yi shiru ne dan yana nazari.

wani kuma kawaicin sa shine maganar sa.



      ~9-Rayuwa tana koya maka so, yau da gobe na koya maka wa kake so, matsalolin rayuwa na koya maka wa ke son ka.




     ~10-Da tausasawa ake bude dukkan kofofin soyayya.



      ~11-.A lokacin kuka ake gane masoyi na gaskiya, ba a lokacin dariya ba.



       ~12-Masu hikimar zance sukace: "wani lokacin akwai buqatar kabar wanda kake so, domin neman Wanda yake son ka".




       ~13-Makiyan ka mutane uku ne: Mai kin ka, da mai kin masoyin ka, da mai son makiyin ka.



       ~14-Ka bar wani don Allah, amma kar ka bar Allah don wani.



       ~15-Ba duk Masoyin ka bane yake iya yi maka Nasiha, Amma duk wanda yake maka Nasiha Masoyin ka ne.



       ~16-Kada ka yarda! da wanda ya yabe ka da abin da ba ka da shi, da sunan yana ƙkaunar ka. Idan ƙkaunar ta gushe, zai iya lika maka sharrin da ba ka yi ba.



       ~17-Ba lallai bane ka burge kowa a rayuwa, yayin da wani ke yabon ka, wani kuma zagin ka yake, kai dai kayi iya yin ka kaga baka cutar da kowa ba, da ka cutar gwara a cuce ka.



     ~18-Da a barka da Allah, gwara ka bari don Allah.



      ~19-Idan dan uwanka ya cuce ka, kana da zabi biyu: Ko dai ka rama cutar, ka ji dadi na wani dan lokaci, ko kuma ka yafe ma sa, sai ka ji dadi mai dorewa.



       ~20-Bata wani, ko bayyana gazawar sa a wajen wasu, to hakan na nuni da cewa shi ne ya gaza, domin duk mutumin da yake ƙkokarin bata sunan wani a wajen wasu, za ka ga wanda yake ƙkokarin batawar ya fi shi da wani abu, da shi ya gaza samu.



       ~21-Masu hikimar zance: "sukace ba zaiyu ka farantawa kowa Rai ba, Amma kayi kokari kaga baka cutar da kowa ba.



       ~22-Idan ka ga mutum yana sukar dan uwansa, ba ya ganin na sa aibin, to ko sukar dan uwan sa da yake yi, shi ma aibi ne.



       ~23-Mutum yana rubuta kurakuran sa ne akan ruwa, yana kuma rubuta na wasu akan dutse, shi yasa yafi tuna kurakuran wasu akan nasa.



       ~24-Idan ba ka son a soke ka, kada ka ce komai, kada ka aikata komai. Duk wanda ya motsa dole ne sai an soke shi.



       ~25- Kada ka damu da cewa karya ta mike kafa, Tabbas karya za ta gushe. 

Kada ka damu da tambayar yaushe ne gaskiya za ta bayyana, Lalle za ta bayyana, komai dadewa. Abinda ya kamata ya dame ka shi ne, mine ne matsayin ka? a kan gaskiya ka ke ko a'a?



      ~26- Mala'iku su na da hankali, amma ba su da sha'awa. Dabbobi suna da sha'awa, amma ba su da hankali. Dan Adam ne Allah ya hada ma sa guda biyun. Idan hankalin ka ya rinjayi sha'awarka, ka bi sawun mala'iku. Idan sha'awar ka ta zarce hankalin ka ka shiga sahun dabbobi.



      ~27-Idan ka zabi son rai a kan gaskiya to zaka ci karo da abin da rai baya so



      ~28-Yana daga cikin cikar kamalar mutum shi ne, aikata daidai a lokacin da babu me ganin sa.



     ~29-Daukar cewa baka kuskure, shine mafi German kuskure.



     ~30-Kada ka damu da masu kulla ma ka sharri, duk iya kokarin su ba su wuce zartar da Kaddarar Allah a kan ka ba.


     ~31-Asiri da sharri da mugunta dukkannin su yan aike ne, suna dawowa ga wanda ya aike su.



     ~32-A gurin saurin yabo, akan yabi mugu.


  

    ~33-Kar ka yi mamakin mutumin da ke sauya soyayya zuwa ƙkiyayya bagtatan, ko can farko ba sonka ya ke ba, sai dai ya ƙkware ne a fannin boye hikidi da munafurci, amma yanzu da ya samu dama sai ya bayyanar da abinda ya jima ya na ɓoye maka.



      ~34-Wani mutum idan ka yi ma sa alheri, zai saka ma ka ne da sharri, Idan ka amfane shi zai cuce ka, Idan ka sa shi inuwa zai jefa ka a rana, Kada ka damu, Ka ci gaba da yin alheri, kowa halinsa ya ke yi.



     ~35- Ka daina ganin cewa dole ne a kyautata ma, kamar yadda kai ma kake yi, In kayi haka ka yaudari kanka.



    ~36-Bacin ranka zai iya zama murmushi wani, amma murmushin ka kar ka yadda ya zama Bacin ran wani.



    ~37-Kada ka bari makiyin ka yasan me yasa ka kuka, domin idan ya sani gobe da shi zai saka ka kukan.

 

     

      ~38-Mutane na iya ganin mikin da ke a jikin ka, amma ba za su iya jin zafin da kake ji ba.

   Sirrinbka na ka ne, idan kirjin ka ya kasa rike shi, kada ka zargi wanda ka fada ma shi idan ya yada shi.



    ~39-Ya kamata kayi farin ciki idan kana da mahassada, don hassada Allama ce ta nasara.



    ~40-Daga lokacin daka dauki rayuwa irin ta wane, daga lokacin ka rusa taka.



    ~41-Masu hikima na cewa mutane kala kala ne, Wasu kamar abinci suke, kullum sai an neme su, Wasu kuma kamar magani suke ba'a son haduwa dasu, yi kokari kazama daga cikin wadan da ake nema kullum sabi da kyawawan dabi'un su.



      ~42-Mutuwa gaskiya ce mai daci, rayuwa karya ce mai cike da ado da daukar hankali.



      ~43-Numfashin mutum, takun sane zuwa ajalin sa.



      ~44-Idan ka kwanta baka sani ba wane ne zai tashe ka: Iyalanka ne ko Mala'ikan mutuwa! Ka zama cikin shiri a kullum kada a riske ka.



      ~45-Yau Aiki ne ba  Hisabi ba, Gobe kuma Hisabi ne ba Aiki ba.



      ~46-Mafi hankalin mutane shi ne wanda ya bar duniya kafin ta bar shi, ya gyara kabarinsa kafin ya shige shi, ya yi sallah a cikin jama'a kafin su sallace shi, sannan ya yi ma kansa hisabi kafin a gurfanar da shi a ranar hisabi.



      ~47-Kayi Aikin, ka kyauta aikin don samun sauƙin Hisabin.



      ~48-Rayuwa kamar littafi ce. Kwanukan ka su ne shafukan ta, maganganun ka su ne alkaluman ta, ayyukan ka su ne rubutunta, kai kuma kai ne mai yin rubutun. Abin da ka rubuta a duniya da shi ake yi ma ka hukunci gobe alkiyama.



      ~49-Idan ka kasa gane wurin da ka yi shuka, kada ka samu damuwa, wata rana ruwan sama ne zai nuna ma ka. Shuka alheri ka wuce a can gaba za ka tsince shi.



       ~50- Rayuwa kamar masarace a hannun dan Adam, muddin zaka gwaigwaye ta komai tsumulmularka sai ta kare. 



      ~51-Rayuwa a kullum cikin canji take. Yaro zai girma, babba ya tsufa, mai lafiya ya yi ciwo, wani mai ciwo ya warke, rayayye kuma ya mutu. Lokacin da ka samu, sannan wani zai rasa, idan ka fadi, wani ne zai tashi. Rungumi hukuncin Allah, a cikin amincewa da yarda.



      ~52-Duniya kamar inuwa ce, duk inda kaje zata bika, amma in ka bita zata guje maka, kuma baza ka taba cimmata ba.



      ~53-Duk wanda ya cuci kuruciyar sa, tsufan sa zai cuce shi. Jikin ka abin hawan ka ne, ka lallaba shi, don kada wata rana ya kasa daukar ka.



      ~54- Idan Har zakayi Rayuwa da Gaskiya, to Tabbas zaka rayu da Aminchi, idan Har ka kiyaye gaskiya a Cikin muamular ka, to ko makiyan ka ma Sai sun neme ka.



       ~55-Mutane shida ba su gamawa lafiya:

1. Wanda ya tozarta abokinsa.

2. wanda ya raina mahaifansa.

3. wanda ya wofinta iyalansa.

4. wanda ya muzanta malaminsa.

5. wanda ya ha'inci makwaucinsa.

6. wanda aka yi masa alheri ya saka da sharri.



       ~56-Jin daɗin rayuwar ka, ya dogara da ingancin tunanin ka.



       ~57-Ita rayuwa takan zo wa mutum ne a yadda ya dauke ta, don haka dan uwa yi kokari ka kyautatawa kowa, daga kan fuskar ka har cikin zuciyar ka, domin babu wanda yasan ya rayuwa zata kasance maka ba a gobe.



        ~58-Ita rayuwa zagaye ce, mai nasara yakan Fadi, Mara nasara yayi nasara.



        ~59-In dai ba so kake ka mutu bawa ba, tashi ka nema.



        ~60-mutumin da yake son jin dadin gobe, to dole sai yayi hakuri da juriya a yau din sa.



        ~61-Wani tasannin shi ke koya mana juriya a rayuwa, kamar turare ne, lokacin da garwashi yake kona shi yake bada kanshi me yawa.



        ~62-Karka zama me sarewa sabi da wasu na kalubalantar ka, nasara bata zuwa sai da kalubale. 



         ~63-Sau tari Faduwa ita ce babbar nasara, don zata baka nasarar fahimtar raunin ka.



        ~64-Duk wanda ka gani a cikin inuwa yana sha'anin rayuwar sa cikin alfarma, tabbas rana ce ta zamo jagora a gare shi.




       ~65-Sirrin fara duk wani aiki shi ne: tunkarar manyan lamurra da mai she su kanana.


       ~66-Nasara tana tare da duk wani abu karami ne ko babba, kada ka raina duk wani kokari naka, har sai ka Kai ga nasara.



      ~67-Da yawan kofofin arziki a bude suke, yanke kauna da iya bude su, shi yake hana hana ka shigar su.



      ~68-Ba mai kallon ka a lokacin da baka da komai, don haka kada kaji kunya a lokacin da ka ke nema.

A lokacin daka samu, Nasarar ce zata fitar da Kai.



     ~69-A rayuwa dole sai ka sha rana kake yin rana.



      ~70-Lokaci kamar walkiya ne, ba ya jira, Ko ka ci moriyar sa nan take, ko kuma ya tafi ya bar ka.



      ~71-Kamar yadda agogo yake zagayawa ga sa'o'i daban-daban,  haka tayuwa take zagayawa yanayi daban-daban, idan yau batayi maka dadi ba gobe zata yi maka.



      ~72-Abu biyu neman ka su ke yi: Arziki da Ajali. Arzikin ka ba zai wuce ka ba, kai kuma ba za, ka wuce ajalin ka ba. Kada ka wahalar da kan ka wajen neman abinda ke neman ka, kada ka ji ciwon abin da ka rasa, idan na ka ne zai dawo ma ka, idan ba na ka ba ne dabarar ka ba zata kamo shi ba.



    ~73-Ba zaka iya gujewa kaddarar kaba, kamar yadda ba zaka iya canzata ba.



     ~74-Mu guji roko, domin babu abinda ya kai shi saurin zubar da daraja da Kimar Dan Adam.



      ~75-Idan ka wadatu da halin da kake ciki a rayuwa, sai Allah ya wadata ka da walwala da kwanciyar hankali.



       ~76-Kar ka Bari Zuciyar ka ta rataya da Wanin Allah, domin shine Babban abinda ke jawo Damuwa da baƙin ciki a Rayuwa.



       ~77-Abu 2 idan kana da su kai sarki ne, lafiya da wadatar zuci.



      ~78- Komai a duniya yana da mabudi, Mabudin ilimi shi ne tambaya, Mabudin nasara hakuri, Mabudin arziki tsoron Allah, Mabudin zaman lafiya adalci da gaskiya.



     ~79-Rinjayar mai karfi ba shi ne gwaninta ba, gwani shi ne wanda ya iya bakin sa, ya rinjayi zuciyar sa, sannan ya ji tausayin ma su rauni.



      80-Wanda bai koyi yin biyayya ba ba zai iya zama shugaba nagari ba.

Comments