4.HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN (4)
4.HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN
B*shakz hikayoyi B*shakz
Bayan barawon nan sun gaisa da Ali baba, sai barawo ya ce wa Ali Baba, "Ni farke ne, na zo da man girki ne domin kai wa kasuwa na sayar, ga shi dare ya yi mini ban samu shiga kasuwar ba, ko zan samu alfarmar masauki a wurin ka da kuma wurin da zan sauke kayana kafin gobe da safe na shiga kasuwa?"
Ali Baba ya ce, "Wa zai ki bako? Ai bako rahama ne, Babu komai, shigo da kayanka daga ciki ka sauke kafin Allah ya kai mu gobe. Zan dawo na nuna maka dakin da za ka kwana idan ka gama sauke kayan."
Barawo ya yi ta godiya, kamar mutumin kirki. Ali Baba kuwa ya wuce cikin gida, ya bar barawo ya na sauke kayan sa a farfajiyar gidan.....
CIGABA
Da Ali Baba ya shiga cikin gida, sai ya fada wa matar sa da kuyangar sa Murjanatu cewa ya yi bako. Ya ce, "Farke ne ya zo da man girki zai kai kasuwa ya siyar amma dare ya yi masa, don haka zai kwana a nan gidan tare da kayan sa zuwa gobe da safe. Yanzu zan fita zuwa farfajiyar gidan mu kara gaisawa da shi, a kai mini abinci na can, za mu ci tare."
Suka amsa masa da to. Ya fita.
Ko da ya fita ya tarar da shugaban barayi ya gama sauke kayan sa. Ali Baba ya nuna masa dakin da zai kwana. Barawo ya kara yin godiya, sannan ya ce wa Ali Baba yana so ya nuna masa cikin gari domin bude ido, tun da shi bako ne. Ali Baba ya ce masa to, amma ya dakata sai sun ci abinci tukuna.
Murjanatu ta kawo musu abinci, har ta juya za ta tafi sai Ali Baba ya ce da ita, "Idan mun gama cin abinci za mu shiga cikin gari ni da bakona, akwai kifi na nan na siyo, ina so ki soya mana shi kafin mu dawo daga cikin gari."
Murjantu ta amsa cikin girmamawa, ta tafi.
Bayan Ali Baba da barawo sun gama cin abinci, sai suka tashi suka nufi cikin gari.
Ita kuma kuyanga Murjanatu ta dauko kifi ta nufi dakin dafa abinci domin soyawa kamar yadda aka umurce ta. Bayan ta hura wuta, ta dora tasar suya, sai ta jawo jakar da ake ajiye mai a ciki, sai ta ji ta kwambar babu komai a ciki. Ashe ta manta sauran man ne ta yi abinci da shi. Ga shi dare ya yi ballantana a tafi kasuwa a siyo. Nan take sai ta tuna, "Af! Shin bakon maigida mai ne ya zo da shi domin siyarwa kasuwa ba? Bari na je wurin da ya sauke man, na debo wanda zan soya musu kifin da shi, alabashi idan maigida ya dawo sai in fada masa, sai ya saye jakar man da na diba gaba daya."
Ta dauki abin dibar mai ta nufi inda shugaban barayi ya sauke kaya. Tana zuwa sai ta taba jakar mai daya za ta bude, sai ta ji an ce, "Lokaci ya yi ne?"
Sai abin ya bata mamaki, nan da nan ta gane abin da ake shirin kulla wa maigidan ta, sai ta canja murya kamar namiji ta ce, "Da saura!"
Ta nufi wata jakar za ta buda, sai ta ji an ce, "Lokaci ya yi ne?"
Ta kara canja murya ta ce, "Da saura!"
Sai da ta bi duka jakunkunan nan guda talatin da bakwai, ta gane duka mutane ne a cikin ksu, sai guda daya ce kurum ta ke dauke da mai. Ta ciccibi jakar da take da mai, ta nufi dakin girki.
Da isarta dakin girki, sai ta sauke tasar suyar kifi ta dora babbar tukunya, ta juye man nan gaba daya a cikin tukunyar. Ta tafasa man sosai har sai da ya tafasa. Ta diba yadda za ta iya dauka, ta dauki shantu ta tafi wurin barayin nan. Idan ta je ga jaka sai ta tura shantu a ciki, ta dura tafasasshen mai a cikin jakar, tun barawo na motsi har sai ta ji ya yi shiru, ya mutu. Haka ta bi su daya bayan daya, tana kashe su da tafasasshen mai, har ta kashe su duka. Sannan ta soya kifin da aka ce ta soya.
Lokacin da Ali Baba da shugaban barayi suka dawo daga yawo cikin gari, Murjanatu ta kawo musu kifi suka ci. Da suka gama suka yi sai-da-safe da juna, barawo ya shige dakinsa, bai san abin da ake ciki ba, shi ma Ali Baba ya shige cikin gida.
Ita kuwa Murjanatu da ta shiga dakinta ta rufe kofa, sai ta bude taga tana kallon abin da zai faru a farfajiyar gidan idan shugaban barayi ya gane an kashe masa mutane.
Can da dare ya tsala, gari kowa ya yi tsit, sai Murjanatu ta ga shugaban barayi ya bude dakin sa a hankali ya fito, ya nufi inda jakunkunan mai suke. Ta ga ya taba daya, ya jira bai ji motsi ba. Ya kara taba wata, babu motsi. Ya bi su gaba daya ya taba, babu mai motsi. Sai ya bude daya, domin ya ga ko barci ne ya dauke su. Sai Murjanatu ta ga ya ja da baya cikin alamun jin tsoro. Daga nan sai ta ga ya yi sauri ya nufi kofar fita daga gidan, ya bude, ya arce.
Murjanatu ta mayar da tagar dakinta ta rufe, ta tabbata cewa maigidanta ya tsallake wannan tarko, sai dai ba ta san da wane shiri wancan barawon da ya tsallake zai dawo ba, ko wane irin tarko zai sake kafa wa Ali Baba? Ta kwanta kan gadonta tana jiran gari ya waye ta fada wa Ali Baba halin da ake ciki.
Da gari ya waye, Ali Baba ya fito farfajiyar gidan, domin su gaisa da bakon sa, ga mamakin sa sai ya ga kofar dakin sa a bude, babu bako babu alamun sa, amma kuma ga dabbobin sa nan da kuma hajar sa ta mai. Yana nan tsaye yana mamakin inda bakon sa ya shiga, sai ga kuyangar sa Murjanatu ta fito, ta durku sa ta gaishe shi.
Ya tambaye ta, ko ta ji motsin bakon sa? Domin tagar dakin ta na kallon farfajiyar gidan ne, duk wani motsi da za a yi a farfajiyar gidan Murjanatu za ta iya ji daga cikin dakinta. Ta ce da Ali Baba, "Maigida zo ka duba da idon ka, ka kara yi wa Allah godiya, da ya kubutar da kai."
Ta ja shi har zuwa wurin da jakunkunan mai suke, ta ce ya bude daya da kansa ya ga abin mamaki.
Ali Baba ya bude jakar mai daya, sai ya ga mutum a ciki, rike da takobi. Ya juya zai gudu cikin tsoro, Murjanatu ta dakatar da shi. Ta ce, "Wannan mutum da kake gani ba zai iya cutar da kai da komai ba domin kuwa ba shi da rai. Mutum talatin da bakwai ne, duk Allah ya ba ni nasarar kashe su da tafasasshen mai."
Ta kwashe labarin abin da ya faru duka tun daga lokacin da ta ga ana yi wa gidan su lamba, da kuma yadda ta zo dibar mai a cikin hajar bako, ta gane mutane ne a ciki, da yadda ta kona su da mai, da kuma yadda ta ga shugaban barayi ya bude gida cikin dare ya arce, da ya gano cewa an kashe masa mutane.
Ali Baba ya yi mamaki a kan hikima da kuma dabara ta wannan yarinya, gayar mamaki. Ya gode mata, godiya mai yawa, kuma ya yi mata abishir da wata kyauta mai tsoka, amma bai fada mata ko mene ne ba. Ya tura ta ta kira masa wani bawan sa mai suna Abdallah.
Da Abdallah ya zo, Ali Baba ya fada masa abin da ke faruwa. Ya ce yana so su tafi lambun da ya ke cikin gidan su gina katon rami mai fadi da zurfi, wanda zai iya daukar barayin nan duka, su rufe su ciki. Ali Baba ya taimaka wa bawan sa Abdallah suka gina katon rami, Allah ya taimake su akwai danshi a cikin lambun, saboda haka ba su sha wata wahala ba wurin haka ramin.
Suka rika ciccibo gawar barayin nan, daya bayan daya, suna jefawa cikin ramin duk da jakunkunan da suke ciki, har suka jefa su duka. Suka mayar da kasa suka rufe. Ali Baba ya gargadi bawan nan, duk da yake ya san amintacce ne, a kan kada ya kuskura ya yi wannan zance da kowa a waje. Jakan barayin nan kuwa, sai Ali Baba ya rika dibar biyu, uku, yana tura Abdallah da su kasuwa yana sayar masa, tunda ba wani amfani zai yi da su ba, har suka kare.
Shugaban barayi kuwa da ya gudu daga gidan Ali Baba, sai ya koma maboyar su a cikin daji. Ba da jimawa ba, kadaici da kuma tsoro suka lullube shi, ya ji kwata-kwata ba zai iya zama shi kadai a cikin daji ba. Saboda haka sai ya debi wani abu daga cikin dukiyar nan, ya yi shiri kamar wani bakon alhaji, ya koma cikin gari.
Da ya isa cikin gari sai ya tasar wa fada. Aka yi masa iso gun Sarki, ya ce shi bako ne, sunan sa Koja Husaini, yana so ya zauna a cikin wannan gari idan Sarki ya yarda, idan ma zai samu gida na siyarwa, to zai siya ya zauna a ciki.
Sarki ya sa dillalai suka nemo wa Koja Husaini gida, aka yi ciniki ya biya. Kwamfa! Ashe gidan kuma yana makwaftaka ne da tsohon gidan Ali Baba wanda ya tashi a ciki, ya koma gidan Kasim, wanda kuma yanzu babban dansa ne, saurayi dan kimanin shekaru ashirin da uku, a ciki.
Koja Husaini ya tare cikin sabon gidan sa, lokaci-lokaci kuma yakan koma maboyar su ya debo wani abu daga cikin dukiyar su, wadda yanzu ta zama mallakar sa shi kadai. Amma ya kan yi taka-tsan-tsan duk lokacin da zai tafi, domin kada ya ja hankalin mutane su fara zargin sa. Kullum zuciyar sa cike take da tunanin hanyar da zai bi ya kashe Ali Baba.
Sannu a hankali Koja Husaini ya fara sabawa da makocin sa, dan Ali Baba, duk da yake ba sa'arsa ba ne, har ta kai ga wani lokaci suna zaunawa su yi ta hira a tsakanin su.
Ana nan wata rana sai Ali Baba ya kawo wa dan sa ziyara a gida, a lokacin kuma Koja Husaini na zaune a kofar gidan sa, karkashin wata bishiya, yana hutawa. Da ganin sa, nan take Koja Husaini ya shaida shi. Ali Baba ya shige gidan dan sa, bai ko lura da wani mutum ba, ballantana ya lura da ana kallon sa.
Bayan wani lokaci, Ali Baba ya fito daga gidan ya yi tafiyar sa. Ba a dade ba kuma sai ga dan sa ya fito, da ya ga Koja Husaini zaune a kofar gidan sa, sai ya nufi can domin su yi hira. A cikin hirar tasu ne Koja Husaini ya fahimci cewa wannan yaro, wanda ya zama tamkar abokin sa a halin yanzu, dan Ali Baba ne, babban makiyin sa a duniya. Don haka sai ya raya a zuciyar sa, bari ya ja shi a jika, wata kila ta sanadiyar sa zai cimma burin sa na kashe Ali Baba.
Tun daga wannan rana sai alakar Koja Husaini da Dan Ali Baba ta dauki sabon salo. Koyaushe Koja Husaini ba ya da wani aboki da ya wuce Dan Ali Baba, ya yi ta jan sa a jika har suka shaku da juna suka zama tamkar abokai sa'o'in juna.
Ina ya Allah, babu ya Allah! Ana nan sai matar Ali Baba ta haihu. Tun kafin ranar suna Ali Baba ya shirya wata 'yar gajeruwar liyafa ta cikin gida, watau iyalan sa da barorin sa kawai.
Da Dan Ali Baba zai je wurin liyafar sai ya gayyaci babban abokin sa, Koja Husaini, domin ya raka shi. Koja Husaini ya yi matukar farin ciki a ran sa, damar da yake ta faman jira kwana da kwanaki yanzu ta samu. Idan suka tafi, zai yi iyakar kokarin sa ya kebe da Ali Baba wani wuri, inda babu kowa, ya kashe shi ya gudu, lokacin da duk hankulan iyalan sa suke wurin liyafar. Sai ya dauki wata sharbebiyar wuka ya sulle ta a cikin rigar sa, suka tafi.
Ko da suka isa gidan, komai ya kankama. Dan Ali Baba ya gabatar da abokin sa ga mahaifin sa, sannan suka sami wuri suka zauna. Duka-duka wurin liyafar bai wuce mutum biyar zuwa shida ba; Ali Baba da matar sa, Dan Ali Baba da abokin sa Koja Husaini, Abdallah bawan Ali Baba, sai kuma yarinya Murjanatu da take ta faman kawo kayan ciye-ciye da shaye-shaye.
Murjanatu na cikin rarraba abinci ga mahalarta liyafa har ta zo kan Koja Husaini. Tana ganin sa, nan take kwakwalwar ta, mai kama da kwamfuta, ta gane shi. Shugaban barayin nan ne ya sake dawowa. Tabbas wannan zuwan ma, akwai manufar da ya zo da ita, ba liyafar ce ta kawo shi ba. Ta kanne abin a cikin ranta, ba ta ce komai ba, ba ta kuma nuna alamun komai ba, tana tunanin hanyar da za ta yi maganin wannan barawo.
Bayan liyafa ta kankama, kowa ya fara motsa bakin sa da abin da aka tanadar. Tuni kuma Murjanatu ta gano wata dabara da za ta kashe wannan barawo. Ta rada wa bawan nan Abdallah, ya dauko dundufar sa ya fara kida ita kuma za ta yi rawa, kamar yadda suke yi wa Ali Baba a duk lokacin da yake bukatar nishadi.
Abdalla ya jawo dundufar sa ta kida, ya fara kadawa a hankali, dama kuma gwanin kida ne, ita kuma Murjanatu ta tashi ta fara taka rawa, abin gwanin ban sha'awa.
Al'adar garin ce, idan mace tana rawa a cikin maza, ta kan rike wata 'yar karamar wuka a hannunta. Idan ta yi rawa, ta yi juyi, sai ta zo gaban mutum ta daga wukar nan kamar za ta daka masa ita a zuciya, sai ta juya wukar ta daka masa marikin wukar. Sai a yi tafi, a yi shewa, ta haka ake gane namiji mai tsoro da kuma jarumi. Duk kasar kowa ya san da wannan al'ada, hatta Koja Husaini ya san da haka.
Saboda haka lokacin da Murjanatu za ta fara rawa, sai ta dauko 'yar karamar wuka ta rike a hannun ta, tuni ta ayyana abin da za ta yi a cikin ranta.
Ta fara rawa tana juyi, ta zo kan mai kida, Abdallah, ta daga wukar kamar za ta daba masa ita, sai ta daba masa kotarta, aka yi tafi. Ta wuce wurin Dan Ali Baba, ta yi kamar yadda ta yi wa Abdallah, ta wuce. Ta je kan Shugaban barayi, ta daga wukar nan, ta tattara iyakar karfinta a hannunta mai wukar ta kirba masa ita a kahon zuciya.
Nan take barawo ya fadi kasa yana shure-shure har ya mutu.
Ko da Ali Baba da dansa suka ga wannan danyen aiki da Murjanatu ta aikata, wanda ba su san dalili ba, sai suka taso mata, hankalin su a tashe, suka far mata da fada, don me za ta kashe bakon da suka gayyato, laifin me ya yi mata.
Murjanatu ta dakatar da su, sannan ta bayyana musu ko wane ne wannan bako, sannan ta ce musu, "Duk da yake ban san manufar da ya shigo da ita wannan gida ba, amma na tabbata manufar sa ba ta alheri ce ba."
Da suka duba jikin shugaban barayi, sai suka samu sharbebiyar wuka sulle a cikin rigar sa. Wannan shi ne karo na biyu ke nan da Murjanatu ta kubutar da rayuwar Ali Baba daga halaka.
Saboda haka yanzu ne zai sanar da ita albishirin da ya boye mata a cikin zuciyar sa, wanda kuma ya taba furta mata.
Ali Baba ya dubi Murjanatu ya ce, "Daga yau na 'yanta ki, kin zama 'ya mai cikakken iko, kuma idan kin yarda ina so ki amince da dana ya zama mijinki."
Sannan ya juya wurin dan sa ya ce da shi, "Ya kai dana, na san da cewa ba za ka ki amincewa da zabina ba, ka amince na aura maka Murjanatu domin na tabbata ta dace da kai, kuma ba domin ita ba da wannan abokin naka ya sami galaba a kaina, dama ya yi kokarin yin abota da kai ne domin ya samu ya kashe ni. Na tabbata da bukatar sa ta biya, kai ma ba zai bar ka ba. Don haka wannan yarinya ita ce sanadiyar kubutarmu gaba daya."
Murjanatu da Dan Ali Baba suka amince da junan su. Bayan 'yan kwanaki aka daura musu aure, aka sha biki aka watse, mutanen gari suka yi ta sa albarka, a kan wannan karimci da Ali Baba ya yi wa yarinya Murjanatu, ga ta baiwa amam ya 'yanta ta kuma ya aurar da ita ga dansa, da ma yarinya ce mai ladabi. Duk mutanen gari babu wanda ya san abin da ya faru.
Ali Baba bai kara komawa maboyar 'yan fashin nan ba, domin yana gudun ya hadu da sauran barayin nan biyu da bai san abin da ya same su ba. Da aka shekara ya ga babu wata barazana da barayin nan suka kara yi masa, ran nan sai ya shirya ya faki idon mutane ya dare saman dokin sa, ya nufi dajin. Ya debo dukiyar ya aza kan dokin àsa ya hawo ya dawo.
Haka Ali Baba ya ci gaba da zuwa dajin nan daga lokaci zuwa lokaci, yana debo dukiyar da barayin nan suka tara yana kawo wa gida, sai dai duk lokacin da ya je yakan yi sauri ya diba ya dawo don tsoron kada sauran barayin biyu su tarar da shi. Ya ci gaba da yin haka tsawon shekaru, ya kwashe dukiyar duka ya kawo gida, kuma yana ci gaba da kasuwancin sa a kasuwa, don haka babu wanda ya san sirrun su. Ya zamana babu mai arziki duk fadin kasar kamar Ali Baba.
Yayi zaman sa shi da iyalin sa cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har mai rabawa ta zo ta raba su.
WANNAN SHINE KARSHEN HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN.
B*shakz hikayoyi B*shakz

Comments
Post a Comment