Musha dariya part 2

B shkaz


Musha dariya part 2.

 Kamar yadda muka fara, yanzu ma zamu kawo muku labarai mask nishadantarwa, insha Allah.



 5-LABARIN SARKIN BADA DARIYA!! .

A wani gari anyi wani mutum, wanda ya shahara wajen bada labarin abin dariya.

 a sabi da haka ne sarki ya bashi sarautar SARKIN BAN DARIYA, na garin, domin yana matukar son labarin ban dariya.

 wata rana, sai sarki ya lura, cewa kwana biyu baya ganin sa a fada. Sai sarki yasa a kirawo shi aji ko lafiya, aka kira shi har fada, sarki yace: "kwana biyu lafiya?" 

 Sai yace "Allah ya taimaki sarki, na zauna a gida ne, domin tattaro basira ta gaba daya, ina rubuta wani labarin ban dariya, wanda duk duniya babu wani mahaluki da ya taba bada labari makamancin sa". 

 ya kara da cewa: daga shi bazai kara bada wani labari ba, har ya mutu. 

 Sarki yayi farin ciki da jin haka, tare da tambayar sa yaushe zai kammala? Sarkin ban dariya yace Ranar kasuwar garin, zai zo ya bada labarin, sarki yace: "Allah ya kaimu". 

 Sarkin ban dariya ya tafi gida, ya cigaba da rubuta labarin shi, har Allah ya kawo ranar, dama sarki yasa anyi shela har garuruwan makwabta duk sun hallara, ana jiran fitowar Sarkin bada dariya. 

 Sarkin bada dariya yayi wanka, ya shirya, har zai fito sai yace: "bari na dan karanta labarin kafin na fita".

 Ya dakko takarda ya fara karantawa, ai kuwa sai ya fasha da dariya, dariya yake, dariya yake, har yakai numfashin sa ya fara daukewa, yanata dariya, kawai sai ya shide, a take ya fadi ya mutu.

 jim kadan sai babban danshi ya shigo domin ya sanar dashi cewa ana jiransa, kawai sai ya tarar da baban shi a mace, ga takarda a gefen sa, sai ya dauki takarda ya fara karantawa, shima yana fara karantawa sai ya fashe da dariya yi yake, shima saboda masifar dariya a take ya fadi mutu. 

 To da sarki yaji shiru bai zo ba, sai ya turo wani bafade yazo ya kira shi, shima bafade ya gansu a mace, ga takarda a gefen su, sai ya dauka ya fara karantawa, shima yana fara karantawa sai ya fashe da dariya har saida ya shide, shima a take ya fadi ya mutu.

da sarki yaji shiru kuma ya kosa yaji wannan labari, sai ya taho da kansa don yaji mai ya faru? yana zuwa sai yaga gawa uku a kwance ga...

 6- LABARIN GOGA DA MALAMINSA

 A makarantar su goga Malam su ya shigo aji Yana koyar da hausa language.

Bayan malam ya kammala bayanai akan JIMLA sai yace to "zan yi gwaji, don naga idan ko kun fahimta".

 Yace "waye zai iya, idan na kawo masa jimla, sai ya kawo min kishiyar ta"?? 

Sai goga yace shi zai yi, sai malam ya fara tambaya kamar haka:- Malam yace: "SAMA" 

Goga yace: "kasa" 
Malam yace: "Ruwa" 

Goga yace: "iska" 
Malam yace: "wuta" 
Goga yace: "Aljanna"
 Malam yace: "malami"
 Goga yace: "dalibi" 
Malam yace: "mai kudi" 
Goga yace: "talaka" 
Sai malam yai murmushi yace: "amma kana dakokari" 
Sai Goga yace: "amma kai dakiki ne" 
Sai malam yace: 
"To ya isa haka" 
Goga yace: "bai isa ba"
 Malam yace: "kana da hankali kuwa"? Goga yace: "mahaukaci ne kai"?
 Malam yace: "dan ubanka kai shuru" 
Goga yace :"dan uwarka kai magana" 
Malam ya kara cewa: "nace kai shuru" 
Goga yace: "nace kai magana"
 Malam yace: "lallai yau zanci ubanka" 
Goga yace : "lallai gobe zanci uwarka"

 7- LABARIN WASU MATAFIYA DA ALJANI A SAHARA

 Wasu mutane ne su (3), suna tafiya sahara, ko wanne daga cikin su ya galabaita, da yunwa da kishirwa, sun wahala matuka, Gashi ko alamar gari basu ganiba, basusan lokacin fitarsu daga wannan saharar ba.

 Don haka harcsun fara tunanin mutuwa. 

 kwatsam! sai ga wata kwalba🧴 a gaban su, su kayi tunanin ruwa ne acikinta, Amma suna bude kwalbar wani hayaki ya tashi sama, hayakin nagama fita, sai ya hade waje daya, sai ga wani Aljani kato agaban su. 

 Nan take aljanin yayi wata mahaukaciyar dariya, yace: "ko wanne acikinku ya fadi bukatar sa ko wacce irice, zan biya masa, sakamakon budeni da kukayi daga wannan kwalba". 

 Ai kuwa sai farin ciki񕱹a rufe su gaba daya, sai aka tambayi ta farko: "mai kike so"?

 Sai tace: "ina so a kaini “DUBAI, a bude min kasuwanci, sannan acikamin katuwar kwantena da kudi a kusa da shagwan kasuwanci na". 

 Sai aljani򇰍yace: "ba wata"?

 Rabi tace "eh".

 Sai Aljani yace "to shike nan rufe idon ki"

 Tana budewa ta ganta Adubai, dukkan abubuwan da ta bukata. 

 Sai aka zo kan tabiyu 2 "Me kike so"? 

Sai tace "a kai ni America, ayi min katon gida, da motoci, da kudi masu yawan da bazan iya karar dasu ba".

 򜔔Aljani򇰍 yace "bawani"? tace "eh". 

Aljani yace: "rufe idonki"

 Tana budewa, ta ganta a America da duk abinda ta bukata. 

 Sai aka zo kan ta karshe "Me kike so".  

Tace "A kawo Min ruwa". 

 aka kawo tasha, ta wanke jikinta. 

 Sai aljani yace: "sai mai kikeso"?

 Sai tace "bukata ta ta karshe A dawomin da ‘yan uwana mucigaba da tafiya". 

 Aljani yace: "itace bukatar ki ta karshe"? 

 Tace: "eh".

 Tana rufe bakin ta sai ga kowacce an dawo da ita, cikin sahara Aljani ya bace ya tafi. 

 8- KARKA YARDA ACE MAKA JAKI. 
Wata rana dabbobi sun hadu suna hira. 

sai zomo ya bada labarin ban dariya aka yi ta dariya ana shewa amma fa shi JAKI bai yi dariya ba, hasali ma sai ya hade fuska ya sha kunu ya bata rai, har aka gama hira, aka watse, kowa ya ya tafi gida.

Bayan shekara guda, zomo ya zo zai wuce, sai yaga JAKI a karkashin bishiya, sai tuntsura dariya yake yana faduwa akasa yana shewa. 

 Zomo ya dubi JAKI yace: "JAKI me aka yi ne kake dariya" ? 

 Sai JAKI yace: "ka tuna labarin nan da ka bayar shekara guda da ta wuce, aka yi ta dariya ni ban yi dariya ba" ??

 Sai zomo yace: "Eh Na Tuna"!. 

 Sai JAKI yace ''to ai ni sai yanzu na gane abinda ake nufi, shi ne nake ta yin dariya yanzu"

 9- HIRAR WANI MIJI DA MATAR SA Wani nmiji ne Matarsa ta ce: “Kwana biyu na rabu da ganin abokin ka Abdul a gidan nan, Allah ya sa dai lafiya”

 Sai ya ce: “Mun ɗan samu saɓani da shi kwana biyu, amma zamu shirya.” 

Sai ta ce: “Allah Sarki...! Abdul mutumin kirki, nasan yanzu haka laifin ka ne, ƙkila kai ne ka ɓata mishi rai.” 

Sai ya ce “ A'a ko kaɗan!, ce mishi nayi ina so in sayi mota, da ƙkuɗin da na samu na siyasar bana, shi kuma yake bani shawara, wai aure yakamata in kara tunda na samu dama, Na nuna kin amincewa ta da shawarar shi, shi kuma yaji haushi, ya ce kwata-kwata bana son ɗaukar shawarar shi, tun daga nan ko na kira a waya baya ɗauka.” 

 Sai ta ce “ Ƙkyale ɗan banza!, Nifa dama kaf! a cikin abokan ka sam! ban yarda da wannan mai ruwan munafukan ba.”
Hhhhhh

10- LABARIN SHEHU JAHA .

 Wata rana Shehu Jaha ya dawo daga kasuwa akan jakinsa. 

 Sai wasu samari suka ce: “Bari yau dai mu zolayi Shehu, muji ko me zaice” . 

Sai suka ce da Shehu: "Shehu bamu sanka ba, amma mun san jakin ka.” . 

Bada wani bata lokaci ba, sai Shehu ya basu amsa da “ai dama su jakuna junan su kawai suka sani.” 


Mun gode da bibiyar mu  fatan kunji labaran, kuma kunyi nishadi.

Mu kasance a musha dariya part 3, don my kara nishadantuwa.

Comments

Popular Posts