2.HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN ( 2)
B*shakz hikayoyi B*shakz
HIKAYAR ALI BABA DA BARAYI ARBA'IN 2
Da barayin nan suka zo gindin dutse sai suka ga jakai guda goma a daure, suka duba ko'ina ba su ga mai su ba.
Sai jikin su ya ba su, domin ba su taba sa ran wani dan Adam zai iya zuwa cikin wannan daji ba, kuma har gindin dutsen su.
Babban su ya matsa gaban dutsen ya ce, "Fayau, bude dutsen Simsim."
Nan take dutse ya bude...
CIGABA
Kofa na budewa, sai Kasim ya fito waje da gudu, ya bangaje wasu daga cikin barayin nan.
Kafin ya sake daga kafar sa wani daga cikin barayin nan ya raba shi gida biyu da takobin sa, gaya-wa-jini-na-wuce.
Barayin nan suka shiga cikin dutsen, suka ga mangalolin da Kasim ya cika da dukiyar su.
Kuma suka lura da cewa lalle ko bayan wannan dukiyar da Kasim ya dauka, akwai alamun an taba dibar dukiyar, ke nan ko Kasim din ne ya taba diba yanzu ya dawo ya kara, ko kuwa akwai wani bayan Kasim din wanda ya dibar musu dukiya.
Suka yi mamakin yadda Kasim ya san kalmomin da ake fada dutsen ya bude.
Domin su gargadi duk wani mai zuwa yana dibar musu dukiya, sai suka raba gangar jikin Kasim gida hudu, suka manna kowanne sashe daya a bango daya na dutsen, watau kudu da arewa, gabas da yamma.
Suka fita suka kora jakunan sa zuwa inda suke tara dabbobin da suke satowa.
Da dare ya yi matar Kasim ba ta ga ya komo gida ba, sai hankalinta ya fara tashi.
Ta dauki mayafinta ta ruga da gudu zuwa gidan Ali Baba.
Ta same shi yana zaune yana hutawa.
Bayan sun gaisa, sai ta ce masa, "Ya kai dan uwan mijina, na san cewa kana da labarin mijina ya shiga daji da jakai, tunda assalatu, akan zai samo wani abu a can, wanda bai fada mini ko mene ne ba. Ga shi har dare ya yi bai komo ba. Shi ne na zo gare ka na ji ko ka san wurin da ya tafi? Ina jin tsoro, ko wani mummunan abu ya faru da shi"
Ali Baba ya ce da ita, "Haka ne, dan uwana ya fada mini zai shiga daji, ai na dauka ya dawo, amma bari yanzu na shirya na tafi neman labarin sa. Ki koma gida zan sanar da ke abin da ake ciki idan na dawo."
Ali Baba ya tashi cikin daren nan ya daura wa jakan sa uku mangaloli, ya kora su ya nufi cikin dajin da dutsen 'yan fashin nan ya ke.
Can zuwa tsakiyar dare ya isa inda dutsen sihirin ya ke.
Da isar sa gaban dutsen ya haska fitilar sa, sai ya ga jini faca-faca ko'ina a gaban dutsen.
Tun daga nan sai ya sha jinin jikin sa. Ya ce, "Fayau bude dutsen simsim."
Nan take kofa ta bude, ya shiga ciki.
Da shigar sa sai kofa ta rufe, ya haska fitilar sa, sai ya ga gawar dan uwan sa Kasim, an datsa ta gida hudu, an manna kowane datse a bangon dutsen.
Nan take ya yi sauri ya harhada su wuri daya.
Sannan ya kuma dibar dukiyar da jakan sa biyu za su iya dauka, ya fita daga cikin dutsen. Ya dora wa jakin sa daya gawar dan uwan sa, sauran biyun kuma ya dora musu dukiyar da ya diba, ya samu kiraren itatuwa ya rurrufe mangalolin da su, yadda mutane ba za su gane abin da aka dauko ba, ya kora su da sauri ya nufi gida.
Can zuwa da hantsi Ali Baba ya isa gida, ya shiga da jakan sa biyu masu dauke da dukiyar cikin gida, ya fada wa matar sa ta sauke kayan ta boye su inda suka boye na farko, ya kora jakin daya zuwa gidan matar dan uwan sa.
Da ya isa gidan sai ya kwankwasa kofa. Bayan kwankwasawa ta biyu, sai ya ga Murjanatu ta bude kofar.
Murjanatu ta kasance baiwa (kuyanga) ce ga kasim, Allah ya hore ma ta tsananin wayo da dabara, duk da ta kasance yarinya karama, mai kananan shekaru, amma hankalin ta da tunanin ta ya zarta na manyan mutane. Shi ya sa ma duk wata shawara da ita Kasim ya ke yi.
Ali Baba ya kora jakin sa cikin gidan, Murjanatu ta mayar da kofa ta rufe, ya umurce ta da ta kira masa matar dan uwan sa. Bayan sun koma, ya sauke gawar Kasim ya shaida musu abin da ya faru da Kasim duka. Bayan sun gama yan koke-koken su, sun share hawaye, sai ya ce musu, "Abin da na ke so da ku shi ne, ina so mutanen garin nan su tabbatar da cewa dan uwana ya mutu ne a gida, a kan gadon sa, sanadiyyar rashin lafiya, ba na so kowa ya san abin da ya faru da shi."
Abin da ya sa Ali Baba ya fadi haka kuwa shi ne, ya tabbata idan barayin nan suka koma maboyar su ba su ga gawar Kasim ba, za su shiga binciken wanda ya zo ya dauke ta.
To idan mutanen gari suka san gaskiyar labarin yadda Kasim ya mutu, da yadda aka rufe gawar sa guntu-guntu, labarin ba zai boyu ga barayin nan ba, kuma za su yi saurin gane Ali Baba su kashe shi.
Amma idan mutanen gari suka san cewa Kasim ya mutu ne a kan gadon sa sanadiyyar rashin lafiya, kuma an yi jana'izar sa gaban mutane, shi ke nan babu wanda zai koma ta kan batun. Don haka babu yadda za a yi barayin su gane wanda ya dauke gawar.
Bayan Ali Baba ya tafi, sai matar Kasim ta ce da Murjanatu, "Na bar wannan a hannunki, ke kika san dabarar da za ki yi, ki kawar da hankalin mutane har su dauka cewa Kasim ya mutu ne sanadiyyar rashin lafiya a kan gadon sa."
Murjanatu ta ce, "Wannan abu ne mai sauki a wurina." Sai ta ruga da gudu zuwa shagon wani mai sayar da magunguna, hankalin ta a tashe, ko takalmi babu a kafar ta, ta ce da shi, "Don Allah yi sauri ka bani maganin zazzabi, ubangiji na Kasim na can zazzabi mai zafi ya rufe shi, har ba ya iya gane masu zuwa wurin sa."
Mai magani ya dauko wani magani ya ba ta, ta karba ta ba shi dirhami daya, ba ta ko tsaya karbar canji ba, ta nufi gida da sauri, ta na rike da magani a hannun ta, tana tafe hawaye na fita daga idon ta.
Duk wanda ta hadu da shi a kan hanya, idan ya ga halin da take ciki, ga kuma magani a hannun ta, sai ya tausaya mata, ya kuma gane abin da take ciki na jiyyar mara lafiya.
Ali Baba da matar sa suka dinga Safa da Marwa tsakanin gidan su da gidan Kasim, domin dai su baddalar da mutane a kan cewa wani abu na faruwa a gidan Kasim.
Don haka lokacin da mutane suka ji kuka daga gidan Kasim, tare kuma da labarin mutuwar sa cikin dare ba su yi mamakin hakan ba.
Tun da sassafe kafin Ali Baba ya gama shaida wa mutane labarin mutuwar dan uwan sa Kasim, domin yi masa jana'iza, ita kuwa Murjanatu sai ta nufi shagon wani baduku, dattijo mai suna Baba Mustafa, domin dama dabi'ar sa ce da an fito daga sallar subahi yake bude shagon sa.
Ta same shi a zaune cikin shagon, bayan ta yi masa sallama sun gaisa, sai ta ce da shi, "Baba Mustafa ina da wani aiki da nake so ka yi mini yanzu, amma da sharadi daya."
Ta dauko dinari daya ta danka masa a hannu.
Ya yi sauri ya karbe yana murmushi, dama idon sa idon kudi kamar wuta da auduga ne, ya ce da ita, "Diyata, fadi abin da kike so na yi miki, ko menene idan dai zan iya yin sa, to zan yi miki shi, duk da dai ban san ki ba, ban ma taba ganin ki ba."
Murjanatu ta ce da shi, "Jiya cikin dare barayi suka shiga gidan mu suka kashe mijina, kuma suka sassara shi guntu-guntu, Ina so, a matsayin ka na baduku, ka harhada gawar sa wuri daya ka dinke, yadda za a ji dadin yi masa jana'iza.
Amma da sharadin zan rufe fuskar ka da mayafi ta yadda ba za ka iya gane hanyar da muka bi zuwa gidan ba, kuma ba za ka iya gane gidan ba.
Haka kuma idan ka gama, zan sake rufe fuskar ka na maido ka shagon ka.
Zan biya ka kudi mai yawa, ka yarda da wannan sharadi?"
Baba Mustafa ya ce ya amince. Murjanatu ta rufe masa fuska, ta ja hannun sa har suka isa gidan, ta bude kofa suka shiga ciki, ta ja shi har cikin dakin da gawar Kasim ta ke, sannan ta bude masa ido.
Ta ce ya yi sauri ya hada shi masu jana'iza na nan zuwa.
Nan take kuwa ba tare da bata lokaci ba. Baba Mustafa ya dinke gawar Kasim wuri daya, kamar ba a taba sassara ta ba.
Murjanatu ta ba shi kudi masu yawa, sannan ta rufe masa idanu ta mayar da shi shagon sa.
Aka yi jana'izar Kasim aka gama. ba tare da kowa ya san gaskiyar abin da ya faru gare shi ba.
Su kuma barayin nan bayan kwana biyu suka koma maboyar su, ga tsananin mamakin su sai suka tarar da an dauke gawar mutumin da suka kashe, bayan wannan kuma an sake dibar musu dukiya.
Cikin fushi, bakin sa na kumfa, babban yan fashin ya ce, "Ina rantsuwa da abin da zai kashe ni, hankali na ba zai kwanta ba har sai na nemo wanda ya gane sirrin mu, yana zuwa yana dibar mana dukiya, ko wane ne shi, kuma ko a ina ya ke cikin duniyar nan.
Idan kuwa na same shi zan gana masa azabar da ba a taba yi wa wani abu mai rai irin ta ba, kafin na kashe shi!"...
Al'adar garin ce idan mutum ya mutu, 'ya 'yan sa ne za su gaji dukan dukiyar sa, idan kuwa ba shi da 'ya 'ya, to 'yan uwan sa ne za su gaje shi, idan babu kuma sai matar sa ta gaje shi, idan ba shi da mata sai a saka dukiyar sa a baitulmali.
Bayan mutuwar Kasim, kasancewar ba shi da 'ya 'ya, sai Ali Baba ya gaji dukan dukiyar sa, da gidan sa, da kuma kuyangar nan tasa mai tsananin hikima, watau Murjanatu.
Ali Baba ya kwashe dukan dukiyar da ya samu daga taskar 'yan fashin nan, ya koma gidan Kasim tare da matar sa. Ita kuma matar Kasim ta koma gidan mahaifin ta.
A cikin wannan halin ne barawon nan ya hilaci dattijo Baba Mustafa, har ya kawo shi gidan da Ali Baba ya ke ciki da matar sa da kuyangar sa.
Kuma ya yi wa gidan 'yar alama da bakin fenti yadda idan suka dawo cikin dare tare da sauran barayin za su yi saurin shaida gidan.
Bayan barawo ya koma wurin 'yan uwan sa, cike da farin cikin gane gidan Ali Baba, ya shaida musu cewa bukata ta biya.
Barayi suka yi murna da wannan labari, Babban su ya ce, "Kowa ya zauna cikin shiri, domin yau cikin dare za mu tafi mu kashe wannan mutum, sannan mu kwashe dukan dukiyar da muka samu a cikin gidan sa." Barayi duka suka shirya suna jiran dare ya yi.
ZAMU CI GABA IN SHA ALLAH
B*shakz hikayoyi B*shakz

Comments
Post a Comment