5.DUNIYAR CRYPTO CURRENCY/ CRYPTO CURRENCY WORLD Tarihin crypto currency (3)
B*shakz
YANAYIN TAFIYAR BITCOIN
~Shi Coin din Bitcoin ko BTC ana hako shi (Mining dinsa) ne da manya manyan kayan aiki, Injuna (Gadgets) masu girman gaske, kuma wajen da ake hako (Mining) din Bitcoin yakan fi girman Filin Ball (Stadium).
~kuma yana zukan wutar lantarki mai yawa, yana jawo dumamar yanayi, da zafi ko Tururin duniya (Global Warming).
kamar yadda kamfanoni da masana'antu suke fitar da hayaki da iska mai zafi suna gurbata yanayi (weather).
B*shakz
~Ana Mining din Bitcoin ne da wani technology da ake kira Proof Of Work, ko kuma (POW), sannan Bitcoin yana da yawan 21 Billion ne kawai, ba kowa ne zai iya mallakar guda daya ba, saboda kudin da aka zuba masa ya juya shi zuwa Abu me tsananin tsada.
~BlockChain dinsa ba a iya gina Smart Contract sosai akan sa, wato ba'a iya kirkiro wani Coin ko token akan Bitcoin chain. Kuma ba'a dora masa wasu aiyuka.
B*shakz
~Bitcoin BlockChain yana iya yin Transactions guda hudu da digo shida a kowane dakika (Seconds) wato (4.6 transaction per second). Sabi da haka muna cikin zamanin sauri da gaggawa ne, BlockChain din Bitcoin ba zai kawo mafita ma duniya ba idan zasu yi amfani da Bitcoin.
~mamaya wato (Bitcoin Dominance), ya mamaye kasuwar, yafi kowa karfi, idan ya fadi sai komai ya fadi, idan ya tashi sai komai ya tashi. manyan masu kudin duniya suna juya kasuwar Crypto yadda suka ga dama, irin su Elon Musk. wannan yasa ake ganin har yanzu crypto bai zo da (yancin hada-hadar kudi (Financial Freedom) da ake zato ba.
B*shakz
Bayan kaddamar da bitcoin zuwa January na 2021 akwai kusan kamfanoni 2,000 na crytocurrencies. Wanda aka fi sani a cikinsu shi ne ‘Bitcoin’. Ragowar kuma ana kiransu da ‘Altcoins’ ko ‘shitcoins’, wadanda suka hada da ‘Ethereum’, ‘Litcoin’, Ripple, Stellar’, Chainlink, ‘Bitcoin Cash’, da sauransu. Yawancin su sun samo asali ne daga fusahar Bitcoin din.
Kuma fasahar Bitcoin yazo da wasu matsaloli, wanda ba za a dauko hanyar magance su ba sai an fara magance batun liquidity a Crypto market, kuma sai an sake sabon gyara ko Ginin Bitcoin, da sauran coins wanda hakan ba zai taba yiyuwa ba.
Don shi tun farko Block Chain Technology baya karban komai sai dai dai da tsarin sa, tsarin da aka daura shi akai tun farko, kuma idan ya karba babu wanda zai iya dakatar dashi har wanda ya kirkiro tsarin.
Sai dai dukkanin wadannan kudaden na internet (crypto currencies) suna bawa mutane dama su yi huldar kudade kai tsaye, ba tare da wani banki ko kamfani ko wani mutum ya shiga tsakaninsu ba, Ana masa taken "Peer-to-peer”!
A wannan lokacin, bincike yana nuna cewa Bitcoin su ne kan gaba da fiye da kaso biyu bisa uku na dukan mu'amallar juya kudaden internet (crypto currencies)
Insha Allah a rubutu na gaba zamu daura akan; CANJIN TAFIYAR KUDADEN INTERNET (CRYPTO CURRENCIES)
B*shakz


Comments
Post a Comment