1.DUNIYAR CRYPTO CURRENCY (CRYPTO CURRENCY WORLD). MENENE CRYPTO CURRENCY
B*shakz
1.DUNIYAR CRYPTO CURRENCY/ CRYPTO CURRENCY WORLD
Abubuwan 12 da rubutun yake dauke dashi
1~Menene crypto currency?
2~Menene blockchain?
3~Menene Mining?
4~Su wanene pioneers?
5~Ta yaya coin yake zama kudi?
6~Menene kasuwancin kudaden Internet (crypto currency)?
7~Tarihin crypto currency
8~Yaushe aka fara Tunanin Samar da kudaden Internet (crypto currenc) ?
9~Kokarin Samar da kudaden internet (crypto currency)
10~Kudin internet (crypto currency) na farko
11~Yanayin tafiyar bitcoin
12~Canjin tafiyar kudaden internet (crypto currency)
13~Canjin da pi network ya kawo wa crypto currency
MENENE CRYPTO CURRENCY
kalmar Crypto asalin ta kalmar Girkawa ne (Greek Word), tana nufi "Secret" ko "Hidden", abin nufi "Sirrance" ko "Rufaffe", daga nan aka samo kalmar Crypto da ma'anar ta, dalilin da yasa aka ba ma kudin Online wannan suna shine saboda tsarin yadda aka shirya kimiyyar gudanar dashi, akan wani tsari da ake ce ma "Block Chain Technology", ko "Kimiyyar da take jere akan tsari hawa-hawa kamar bulo".
B*shakz
MENENE BLOCKCHAIN
Blockchain ta samo asali daga kalmomi biyu ne (Block da Chain) kalmar farko "Block" wato Bulo dai daka sani da Hausa Wanda ake Gini (Gina) dashi, na biyu kalmar "Chain" wato "Sarqa" ko jerin 'kulli.
Idan ka hada su sai kace "Blockchain" wato a gundarin fassara (jerin Bulo, wani akan wani, ko wani biye da wani), shine Blockchain.
B*shakz
an kira shi da Blockchain ne saboda tsarin da Computer take bi domin samar da bayanan da Adana su (Data). tana yin sa ne da tsarin Bulo ko Block, wani akan wani, idan suka yi yawa sai ka gansu a jere kamar Sarka (Chain).
Daga wannan sai wannan, daga wancan sai wancan, haka suke bi.
Shi Block Chain Technology baya karban komai sai dai dai da tsarin sa, toh idan ya karba kuma babu wanda zai iya dakatar dashi har wanda ya kirkiro tsarin..
Haka zai yi ta tafiya duniya tana amfana dashi Koda masu shi sun mutu ko sun watsar dashi
shi Block Chain Technology an tsari ne ta yadda ba'a iya canza bayanan dake cikin sa da zaran an shigar, kuma ba'a iya sace shi, ko hacking din sa ko ayi masa kutse saboda tsaron da aka saka masa.
Haka kuma tsarin Block Chain Technology yana iya detecting (gano) wanda yayi attempt (yunkuri) zai shige shi da wrong information, kuma ya dakatar da mutum na har abada daga shiga tsarin domin 'dora Coin ko wani information.
Wannan tsarin na Blockchain Technology cumpotoci da suke kan wannan tsari, Sune suke tantance bayanan suna raba su zuwa tsakanin su
Idan computocin sun tabbatar da bayanan sai su raba, Kuma su zartas,yadda aka tsara aikin Blocks din da farko, ko dai an tsara suyi aiki da yawa da gaggawa (Scalability), ko kuma sabanin haka.
Dan haka Computers din zasu dinga rarraba bayanan dake kan kowane block, don tabbatar da Mathematical calculation din dake cikin na gaskiya ne, ya dace da tsarin wanda yake biye dashi da wanda yake kafin sa.
Kuma duk bayanin da yazo to babu wani da yake da ikon dakatarwa, an cire Third party, babu wata hukuma da zata binciki wannan tsarin.
shi Block Chain Technology anyi shi saboda duk wata harkar ajiye bayanai ta Online ne a duniya, sai dai harkar kudin Crypto Currency ta sanya mutane da dama basu san cewa block chain Technology bai tsaya akan harkokin kudi kadai ba.
Insha Allah a rubutu na gaba zamu daura akan; MENENE MINING?
B*shakz


Comments
Post a Comment