4.DUNIYAR CRYPTO CURRENCY/ CRYPTO CURRENCY WORLD TARIHIN CRYPTO CURRENCY (2)
B*shakz
KUDIN INTERNET NA FARKO (crypto currency)
Kudin farko da aka samar shine "Bitcoin", an kammala aikin a 2008, sannan aka kaddamar dashi a 2009.
Wanda ya samar dashi shine masanin harkar internet kuma 'dan rajin neman Financial Freedom a duniya, wanda aka ce sunan sa "Satoshi Nakamoto", wasu kuma sunce Babu takamaimai a kan haka, Ana zaton mutum daya ne ko kuma gungun wasu mutane da sunan Satoshi Nakamoto.
B*shakz
Kalmar ‘Bitcoin’ kalmomi biyu ne na turanci a hade. ‘Bit’ tana nufin kadan ko gutsure. ‘Coin’ kuma tan nufin tsabar kudi masu kamanni da kwabo ko kwandala.
An gina lissafi na'urar juya kudin ne da lissafin Computer na salon Algorithm, Ilimi ne mai muhimmanici, da daya daga cikin masana lissafi Musulmi da aka fi sani da Muhammad bn Musa Al-Khawarizmi (780-850 M.) ya kirkiroshi. Gabadaya tsarin kwanfiyuta ma a kan wannan ilimi aka kirkiroshi.
Tsarin lissafin algorithm akan Computer yana bugawa ne da 'digo ko "Bit", ana ganin daka nan aka samo sunan bitcoin.
B*shakz
A lokacin da aka kaddamar da Mining din Crypto Currency na farko, Mutane da yawa sun tara Bitcoin, a wancan lokacin duniya tayi dariya da habaici ma tsarin a lokacin, an shafe kusan shekaru uku mutane suna Mining din Bitcoin akan Computer, saboda a lokacin babu wayoyin hannu na Android sosai a duniya, daga baya a 2010 aka kaddamar dashi akan farashin $0.0008 a Dollar kowane guda 'daya.
Kowane Bitcoin daya a lokacin yana dai dai da Naira 0.35 wato ko Sile Biyar (Ficika) bai kai ba, amma a hankali da mutane suka karbe shi sai da bitcoin ya taba kaiwa 36,000,000 Naira.
Insha Allah a rubutu na gaba zamu daura akan; YANAYIN TAFIYAR BITCOIN
B*shakz


Comments
Post a Comment