2.DUNIYAR CRYPTO CURRENCY/ CRYPTO CURRENCY WORLD Menene mining?

 B*shakz

MENENE MINING?


Mining kalmace na turanci, a Hausance ana nufin hakowa ko tono wani abu daga cikin wani abu.

Kamar yadda ake hakar arzikin zinare da Allah Ya ajiye a karkashin kasa, ana siyarwa da tsadan gaske.to kamar misalin hakane ake mining coin daga kafar yanar gizo


B*shakz


SU WANE (PIONEERS)?

Sune suke temakawa wajan hakar coin, ta hanyar yin mining. su kuma sunayi ne don ribar Kan su, idan coin ya kafu duk abin da suka tara ya zama kudi da zasu kashe.


B*shakz


TA YAYA COIN YAKE ZAMA KUDI?

Mun sani cewa wannan kudi na takardu da muke rikewa muna sayan abu dashi a asali ba shine kudi ba, jama'a ne da Gwamnati suka yadda cewa ya zama kudi, asalin kudi shine zinare da azurfa wanda ake hakoshi daga karkashin kasa,


Kafin zuwan turawan mulkin mallaka Nigeria, kakannin mu a lokacin suna amfani da "wuri" a matsayin kudi, "wuri" ana samunsa a bakin kogi za'a ganshi karami kamar dutse fari haka, a wancan lokacin sai kakannin mu suka yadda dashi a matsayin kudi, ya zama legal tender bayan tsarin trade by barter da suke dashi 

Amma a yanzu da aka daina yarda dashi a matsayin kudi, bai da wata daraja, sai matsafa da 'yan bori suke amfani dashi.


To kamar haka (pioneers) mutanen da suke (minning) hakar coin suke bashi daraja. Sabi da minning din da suke tamkar sun yarda ya zama kudi ne. Kuma adadani (pioneers) masu mining dinsa, adadadin darajar sa.


Haka zalika bayan ya kafu adadin masu cigaba da karbar sa a matsayin kudi adadin karin darajar sa.


Kuma kamar yadda tsarin banki yazo ya kawar tsarin table payment, hakanan ake sa ran Crypto currency zai zo ya mayar da tsarin banki tsohon yayi.


MENENE KASUWANCIN KUDADEN YANAR GIZO (Cryptobusiness) 

Abin da ake nufi shine siyan coin bayan an kaddamar dashi (launching) kafin ya tashi, sai a ajiye bayan ya samu karbuwa yayi tsada sai a siyar.

ko kuma a siye coin lokacin da ya karye, bayan ya dawo da darajar sa a siyar.

Wannan kasuwanci shine Cryptobusiness kuma yana da riba sosai.


Insha Allah a rubutu na gaba zamu daura akan; TARIHIN CRYPTO CURRENCY (1)


B*shakz

Comments

Popular Posts