3.DUNIYAR CRYPTO CURRENCY/ CRYPTO WORLD TARIHIN CRYPTO CURRENCY (1)
B*shakz
TARIHIN CRYPTO CURRENCY (1)
Crypto Currency kudi ne na Internet anfara mu'amala dashi tun 2009 shekaru 12 da suka wuce.
B*shakz
YAUSHE AKA FARA TUNANIN SAMAR DA KUDIN INTERNET (crypto currency)
An fara tunanin samar da kudin internet (crypto currency) wuraren 1980s, a lokacin masana harkokin internet suke ganin ya dace duniya ta samar ma kanta da harkokin kudaden da ba'a iya ganin su, kuma ba'a iya taba su. Saboda cigaba da amfani da kudaden takarda yana 'kara karya tattallin arziki duniya.
.
gwamnatoci suna kashe kudade masu yawa wurin buga su, da kula dasu idan sun tsufa ko yagewa.
sannan ana saurin gano inda suke hakan zai bada damar saurin sace su.
B*shakz
Sabi da haka a shekarun baya masu kokarin kwato 'yancin 'dan Adam suna cewa ya kamata ace a yanzu mutane sun samu "Financial Freedom" wato "Yancin gashin kai ta bangaren harkokin kudi", ba sai sun jira wata kasa ko wata gwamnati ta amince da kudi kaza ba. Suna cewa saka bakin gwamnati acikin harkar kudi yana danne cibagan duniya da walwalar mutane.
Daga lokacin da aka fito da tsarin transfer din kudi ta waya, daga Account din mutum na banki zuwa wani banki, masana suka tabbatar da cewa tsarin Block Chain Technology zai yi nasara.
B*shakz
KOKARIN SAMAR DA KUDIN INTERNET (crypto currency)
A shekarar 1985 wani Baturen kasar America masanin harkar internet, yayi yunkurin samar kudin Online mai kama da Crypto Currency na yanzu, sai dai kasar Amurka ta kama shi, ta daure shi, daga bisani aka yi zargin ta hallakar dashi.
Tun a shekarun 1990, mutane irin su Nick Szabo suka fara zuwa da wani tunani na kulla cinikayya a kan internet da sunan ‘Bit Gold’. Sai dai abin bai samu yaduwa ba sosai.
Haka nan a 1998 Bernard von NotHaus dan Jihar Hawai a Amurka, ya yi irin wancan tinani ya kirikiro ‘Liberty Dollars’. Amma ya firgita gwamnati don haka sai da aka daureshi a kan wannan aika-aika tasa.
.
A 1998 din dai, gwanaye a kan kwanfiyuta basu daddara ba, sai da wani dan China mai suna Wei Dai ya kirkiro ‘B-Money’
A 1997 wani 'dan kasar Japan ya sake irin wannan yunkurin na samar da kudin Online amma kasar Japan ta kama shi,
A 2007 jami’an tsaro a Amurka suka rufe wata manhaja a kan internet mai suna ‘E-Gold’.
B*shakz
A shekara ta 2008 wani masanin harkar internet kuma 'dan rajin neman Financial Freedom a duniya, wanda aka ce sunan sa "Satoshi Nakamoto", (Babu takamaimai a kan wanda ya fara kirkirar wannan tsari. An zaton mutum daya ne ko kuma gungun wasu mutane da sunan Satoshi Nakamoto) yayi/sunyi nasarar kera kudin Online, kuma ya saka masa suna "Bitcoin".
.
Bayan ya kammala aikin a 2008, sai a 2009 ya qaddamar dashi, wanda shine yayi nasara a karon farko a tarihin duniya, da har aka gagara dakatar dashi.
Sai dai ance Satoshi Nakamoto ya gina aikin sa ne akan wanda 'dan kasar Japan din nan ya faro.
Har yanzu ba'a san fuskar Satoshi Nakamoto ba, sai dai bincike ya nuna cewa suna ne irin na 'yan kasar Japan.
Insha Allah a rubutu na gaba zamu daura akan; KUDIN INTERNET (crypto currency) NA FARKO
B*shakz


Comments
Post a Comment